1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Bashir zai yi zaman kaso na shekaru 2

Abdourahamane Hassane
December 14, 2019

Kotu a birnin Khartoum na Sudan ta yanke hukunci a shari'ar da ta ke yi tsohon shugaban kasar Omar Hassan al-Bashir, inda ta ce ta same shi da laifi kuma zai shafe shekarun biyu a daure.

https://p.dw.com/p/3UnHY
Sudan Khartum | Ex-Präsident Umar al-Baschir vor Gericht
Hoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

A wannan Asabar din ce kotun ta yi zaman ta inda ta yanke wannan hukunci na zaman gidan maza na shekaru biyu saboda samun tsohon shugaban Sudan din da ta ce ta yi da laifi na cin hanci da karbar rashawa, musammun dangane da wasu kudaden da Saudiyya ta bai wa Sudan kusan Euro miliyan 81 wanda Al-Bashir din ya karkata akalarsu.

Wannan hukunci da kotun ta ta yanke, shi ne na farko daga cikin jerin hukunce-hukuncen shari'ar da ake yi al-Bashir din tun bayan da sojojin suka kifar da mulkinsa a cikin watan Afrilu da ya gabata sakamakon zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa da jama'a suka yi  bayan ya kwashe shekaru 30 a kan karagar mulki.