Al-Abadi: "Tutar Iraki za ta kada a Fallujah nan da kwanaki"
June 1, 2016Firaministan Iraki Haider al-Abadi ya yi tsokaci game da cigaban da ake samu a gumurzun da ake yi da nufin sake kwace birnin Fallujah daga hannun kungiyar IS mai ikirarin kafa kasar Islama a Iraki da Siriya. Firaministan ya yi fatan cewa nan da wasu kwanaki kalilan masu zuwa za a kafa tutar Iraki a birnin.
"Burinmu na wannan matakan soji a yanzu shi ne mu rage yawan fararen hula da sojoji da gumurzun zai shafa. 'Yan tarzoma sun bibbine nakiyoyin karkashin kasa da sauran ababa masu fashewa, amma da yardar Allah tutar Iraki za ta kada a Fallujah nan da 'yan kwanaki masu zuwa."
Rahotanni dai sun ce kungiyar IS da ke cigaba da nuna turjiya, tana tsare da dubban fararen hula da take amfani da su a matsayin garkuwar dan Adam a birnin na Fallujah da ya kasance hannunta fiye da shekaru biyu.