Akwai yuyuwar saukar Shugaba Asad na Siriya
August 21, 2012Talla
A wata Ziyarar da ya kai a birnin Mosco na Rasha,mukadashin pramiyan Siriya Qadri Jamil,ya fadawa manema labarai cewar a ci-gaba da neman warware rikicin kasar ta hanyar diplomasiya,gwamnatin zata iya amuncewa da duk wata tautaunawa da 'yan adawa domin kawo karshen rikicin,ciki ya ce har da batun saukar shugaba bashar Al-Assad.
To saidai jami'in ya ce maganar murabus ta shugaban ba zata kasancewa ka'ida ga maganar tautaunawar ba. Wannan sanarwar ta zo ne a daidai lokacain da Amirka ta yi barazanar amfani da karfi idan har Siriya ta yi gigin amfani da makamai masu guba a kan masu tawayen.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu