1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Akwai yiwuwar tsawaita dokar kulle a Jamus

February 9, 2021

Alamu na nuna cewar za a tsawaita dokar kullen corona a Jamus zuwa karshen watan Fabarairun shekarar 2021.

https://p.dw.com/p/3p8WS
Deutschland Angela Merkel verkündet neue Corona-Beschlüsse
Hoto: Hannibal Hanschke/REUTERS

A cewar mambobin jami'iyyarta ta CDU Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za ta bukaci kara wa'adin dokar kullen daga ranar 14 ga watan Fabarairu saboda dakile yaduwar cutar a kasar.

Merkel ta ce za a bai wa makarantun naziri da firamare da shagunan siye da siyarwa da kuma na gyaran gashi fifiko a duk wani sassauci da aka samu domin dakile shiga wani dokar kullen amma bisa sharadin za su bi tsauraran matakan dakile yaduwar cutar.

Hakan dai na zuwa ne gabanin tattaunawar da shugabar za ta yi da shugabanin jihohi 16 a ranar Laraba kan cutar.