1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin 'yan jarida na samu koma ba a Duniya

Abdourahamane HassaneApril 20, 2016

Kungiyar 'yan jaridu na ƙasa da ƙasa Reporters Sans frontière ta ce an samu koma baya sossai a kan sha'anin yanci 'yan jarida a shekara ta 2015 da ta shige a cikin ƙasashen duniya da dama.

https://p.dw.com/p/1IZ9r
Symbolbild Pressefreiheit
Hoto: picture-alliance/dpa

Ƙungiyar ta RSF wacce ta bayyana rahotonta na shekara a yau ta ce dalilian koma bayan da aka samu,na da nasaba ne da gallazawa da 'yan jaridu ke fuskanta a duniya a cikin ƙasashe kamar su Turkiyya da Masar da Burundi da Libiya da Yemen da ma na Turai irisu Poland inda gwamnati ke yin katsa landan a cikin aikin 'yan jaridun

A karon Farko yankin Latine Amirka ya zo bayan Afirka a cikin Ƙasashe 180 saboda aikata kisa a kan 'yan jarida misali Banizuwela ta zo ta 139 yayin da Kwalambiya ta ke riƙe da matsayi 134.