Aikin tawagar sa ido a Siriya ya kare
August 19, 2012Talla
Tawagar da Majalissar Dinkin Duniya ta aika domin sa ido ga rikicin Siriya, ta kawo karshen wa'adinta a Lahadi da misalin karfe 12 na dare. A watan Aprilun da ya shude ne a ka kafa wannan tawagar domin saka ido ga kiyaye tsagaita wutar da manzo na musamman Kofi Annan ya gindayawa bangarorin biyu da ke rikici a kasar. Shugaban tawagar Janar Babakar Gaye dan asalin kasar Senegal,ya bayana cewar tun a cikin watan yuni ne tawagar ta tabbatar da babu mai biyaya ga wannan mataki na tsagaita wuta a kasar ta Siriya inda ya zargi bangarorin biyu da kisan fararen fulla. To saidai kawo yanzu babu wani tabbacin ko Majalissar Dinkin Duniyar zata aikawa da wata tawagar sa ido a kasar.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Usman Shehu Usman