1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin bauta na kananan yara a Burkina Faso

June 12, 2012

A ranar hana bautar da kananan yara, Majalisar Dinkin Duniya tace miliyoyin yaran ne suke gudanar da aiyukan da suka fi karfin su, musamman a kasashe masu tasowa

https://p.dw.com/p/15Cok
Hoto: DW

A yayin da ƙasashen duniya ke bukukuwan zagayowar ranar yaƙi da tilastawa ƙananan yara aikin ƙwadago, ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa da ƙasa ta buƙaci ƙasashen duniya su ƙarfafa matakan yaƙi matsalolin dake addabar ƙananan yara ciki kuwa harda safarar su domin karuwanci da kuma tilasta musu yin aikin ƙarfi. Burkina Faso tana daya daga cikin kasashen da kananan yara suke aikin bauta da yafi karfin su.

Ko da shike ranar Talata ce aka cika shekaru 10 da zagayowar ranar yaƙi da sanya ƙananan yara aikin ƙwadago, amma ƙungiyar ƙwadago ta duniya bayyana taƙaicin ganin cewar har yanzu matsalar ba ta ragu ba, domin kuwa a cewar ta daga cikin yara miliyan 215 dake yin aikin ƙwadago domin biyan bukatun su na rayuwar, rabin adadin na fuskantar bautarwa da kuma tilasta musu ɗaukar makamai yayin rigingimu.

Ɗaruruwan 'yan mata ne a ƙasar Burkina Faso, kamar dai sauran ƙasashen Afirka ke yin aikin ƙwadago tun suna kimanin shekaru 9 zuwa 14, inda wasu daga cikin su ke kokawa game da yanayin da suke samun kansu a ciki lokacin aikin ƙwadagon.

Zenabou Ilboudou, wadda a yanzu shekarunta na haihuwa 20 ne kuma take yin aiki da gidauniyar Terre des Hommes, wadda cibiyarta ke ƙasar Switzerland ta ce ta fara aikin ƙwadago ne tun tana 'yar shekaru 9 a duniya:

Terre des hommes
Aikin bautar da kananan yara a Burkina FasoHoto: Tdh | R. Rorandelli

"Ta ce da misalin karfe 5 na safe za'a tada mutum daga barci yayi ɗan aikace- aikacen cikin gida sannan a bashi kuɗi zuwa cefane wani lokacin ma bayan girkin, Uwargida tace abincin baiyi daɗi ba ta rinƙa yin faɗa wani lokaci har da duka. Wani lokacin ma samun abincin rana jidali ne domin ko mutum ya dafa abincin wani lokacin ba za'a bashi ya ci ba sai dai a bashi dala 20 na CEFA ya je ya nemi abinda zai ci. Gaskiya akwai wahala. Wani lokacin ma a cikin Kischen ake kwana."

Baya ga aikin ƙarfi, akwai 'yan matan dake fuskantar barazanar yin lalata da su, kamar yadda Alima Fogo 'yar shekaru 21 a duniya ta ce ta sha fama da hakan a lokacin da take ƙarama:

"Ta ce Wani lokaci maigida in ya Tafi wurin aiki yakan dawo. Idan ya tarar da matarsa ba ta nan, sai ya fara hirarrakin banza dani kuma ya ce yana buƙatar mu fita in dare yayi, amma ni a kullu yaumin nakan ƙi. Wani lokacin yakan tursasa mini ya ce in na amince a ƙarshen wata zai ninƙa albashi na amma ni gaskiya ƙiyawa nake yi. "

Ba wai 'yan mata ne kawai ke fama da matsalar ba, su ma ƙananan yara na fama da aikin ƙarfi ko dai a gonaki ko kuma a wuraren haƙo ma'adinai, amma ba tare da samun ladar a zo a gani ba.

Kinderarbeit Afrika Elfenbeinküste Kakao Plantage
Aikin kananan yara a gonakin cocoa a Cote d'IvoireHoto: AP

A ƙoƙarin kawo ƙarshen waɗannan matsalolin, asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF da wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa irin gidauniyar Terre des Hommes wadda cibiyar ta ke ƙasar Switzerland suka ɓullo da shirye shirye a Burkina Faso, kamar yadda Herman Zoungrana, babban jami'in dake kula da gidauniyar a Burkina Faso yayi ƙarin haske:

"Ya ce aƙalla muna raka 'yan mata wajen 700 zuwa garuruwansu na asali wasu kuma mukan tura su makaranta. Yanzu haka akwai sama da 100 da muka sa koyon aikin hannu. Akwai kuma waɗanda ke makarantun share-fagen shiga jami'a. "

Duk da ƙoƙarin da ƙungiyoyin ke yi, sun bayyana buƙatar ɗaukar ƙarin matakai domin shawo kan sanya ƙananan yara aikin ƙwadago.

Mawallafi: Köpp/Saleh Umar Saleh
Edita: Umaru Aliyu