1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ahmedinijad ya ce ya na son zuwa kallon olympics a London

May 17, 2012

Shugaban Iran Mahmud Ahmedinijad ya bayyana muradinsa na hallartar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Olympics a birnin London wanda za fara a ƙarshen watan Juli.

https://p.dw.com/p/14xC1
Iranian President Mahmoud Ahmadinejad gestures while speaking at the 25th International Islamic Unity Conference in Tehran February 8, 2012. REUTERS/Morteza Nikoubazl (IRAN - Tags: POLITICS RELIGION)
Iran Mahmud AhmadinedschadHoto: Reuters

Shugaba Ahmedinijad ya ce ya na buƙatar yin hakan ne da nufin kasancewa tare da tawagar 'yan ƙasarsa don ƙarfafa mu su gwiwa wajen samun gagarumar nasara yayin gasar wadda ake sa ran kammala ta a cikin sati na biyu na watan Agusta.

Kawo yanzu dai mahukuntan na Burtaniya ba su bayyana matsayinsu game da sahale wa Shugaba Ahmedinjad ɗin halartar gasar ba domin a cewar kakakin ma'aikatar cikin gida ta ƙasashen waje, ba za su tatauna kan batun zuwan ɗaiɗaikun mutane ba inda ya ƙara da cewar hukumar da ke kula da wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta kowacce ƙasa ce da hakkin gayyatar shugabanta.

Dangantaka dai tsakanin Burtaniya da Iran ta jima da yin tsami saboda abinda Burtaniyan ta kira yunƙurin mallakar makaman nukilya da Iran ke yi wanda ya saɓa dokokin ƙasa da ƙasa.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Zainab Muhammad Abubakar