1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ahmadinejad ya tsaya takarar shugaban kasar Iran

June 2, 2024

A lokacin mulkinsa na wa'adi na biyu a tsakanin shekarar 2005 zuwa 2013, Ahmadinejad, ya yi suna wajen sukar Isra'ila tare da kore faruwar kisan kiyashi na Holocaust.

https://p.dw.com/p/4gXyS
Hoto: Rouzbeh Fouladi/ZUMA/IMAGO

Tsohon shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad ya yi rijistar shiga zaben shugaban kasarda ke tafe. Kawo yanzu 'yan takara 20 ne suka sanar da aniyarsu ta tsayawa takarar kujerar shugaban kasar da aka tsara gudanarwa a ranar 28 ga wannan wata, bayan rasuwar da marigayi Shugaba Ebrahim Raisi ya yi sakamakon hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a watan da ya gabata.

Majalisar koli ta kasar ce za ta zauna ta tantance mutanen da ta amince su tsaya takarar ta shugaban kasa. A zaben shekarar 2021, hukumomin na Iran sunhana Mahmoud Ahmadinejad tsayawa takarar shugaban kasa. Yanzu hankali ya koma kan jin matsayar da majalisar kolin Iran din za ta dauka kan sabunta bukatar tasa.