1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan: Ci gaba da samun agaji

December 30, 2022

Duk da matsayar da gwamnatin Taliban ta dauka a kan ma'aikata mata, Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba za ta janye ayyukan jin kai a Afghanistan ba.

https://p.dw.com/p/4LZ6o
Afghanistan, Kandahar
Hoto: Sanaullah Seiam/Xinhua/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba za ta janye ayyukanta na jin kai da take kai wa kasar Afghanistan ba, duk da dokar haramtawa mata aiki a kungiyoyi masu zaman kansu da gwamnatin Taliban ta yi. Babban jami'in majalisar a Afghanistan Ramiz Alakbarov, ya ce Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji za su ci gaba da kai kayayyakin agaji don tallafawa rayuwar 'yan Afghanistan. A lokacin da yake jawabi bayan sanarwar da kungiyar G7 ta fitar na yin kira ga gwamnatin Taliban ta janye matakin, Alakbarov ya ce al'ummar kasar na matukar bukatar ayyukan agaji. Majalisar Dinki Duniyar za ta kuma aika wasu manyan jami'anta zuwa Afghanistan din nan da 'yan makwanni masu zuwa, domin yin kira ga gwamnatin Taliban ta janye matsayarta kan ma'aikatan mata.