1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Agajin jin ƙai a Sudan ta Kudu

February 4, 2014

Majalisar ƊInkin Duniya ta ce tana buƙatar sama da dala dubbu kimanin Euro miliyan 940 domin gudanar da aikin jin ƙai a Sudan ta udu

https://p.dw.com/p/1B2lx
Südsudan Juba Ausschreitungen UN Flüchtlinge 17.12.2013
Hoto: picture-alliance/AP

Majalisar ta ce tana buƙatar kuɗaɗen ne don taimaka wa mutane kusan miliyan uku waɗanda yaƙin da ake fama da shi tun a tsakiyar watan Disamba shekara bara ya rutsa da su.

Da ya ke yin magana da manema labarai shugaban agajin jin ƙai na MDD a Sudan ɗin ta Kudu Toby Lanzer,ya ce abu na farko da zasu yi da kuɗaɗen shi ne ceton rayuka da abinci da magungunan da kuna sauran kayayyaki na buƙata. Ta yadda ƙungiyoyin agaji zasu iya kai ɗauki ga jama'ar da ke a cikin ƙauyuka kafin saukar damina lokacin da hanyoyin mota ke lalacewa. MDD ta ce fadan ya tilastawa mutane kusan dubu tara barin gidajensu kana wasu dubu goma suka mutu.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Pinado Abdu Waba