1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrika: Cinikin sassan jiki ta barauniyar hanya

Binta Aliyu Zurmi
September 19, 2024

Majalisar Dinkin Duniya a wani rahotonta ta ce cire sassan jikin dan adam ta barauniyar hanya na zama wani babban abun mai tayar da hankali musamman a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/4krkW
DW Sendung Shift | 3D Leber
Hoto: Nottingham Trent University

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido kan miyagun laifuka da safarar kwayoyi ya kiyasata cewar a duk shekara ta hanyar safarar mutane da nufin sace musu wasu sassan jikinsu akan sami makudan kudade da yawansu ya kai dala miliyan 840 ya zuwa dala biliyan daya da dubu dari bakwai a kasashen Afirka da dama.

Kasashen Masar Da Afirka ta Kudu da Libiya da Kenya da kuma Najeriya na a sahun gaban kasashen Afirka da da ke fuskantar matsalar cinikin sassan jikin mutum ba bisa ka'ida ba.

Alamar cire sassan jiki
Hoto: picture-alliance/dpa

Hada-hadar wannan kasuwa na karuwa ne bisa bukatar wasu sassan jikin mutum da ake fama da karancin wadanda za su bayar da shi gami da karanci cibiyoyin kiwon lafiya masu dashen koda.

A shekarar 2020 Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce cibiyoyin dashen koda 35 ne kadai ake da su a nahiyar Afirka

A cewar lauya mai kare hakkin dan Adama da ke Najeriya Frank Tietie mafi akasarin wannan mumunar dabi'a da nasaba ne da talauci.

"Ya ce a Najeriya akwai fargabar cewa talauci shi ne ummul haba'isin wannan dabi'a maimakon kyakyawar manufa ta kokarin ceton rai a kokarin taimaka wa lafiyar wani, lamarin ya kai matakin annoba, amma duk da haka al'umma na nuna masa halin ko in kula"

Aikin dashen kodar Alade a wani asibiti a New York
Aikin dashen kodar Alade a wani asibiti a New YorkHoto: Joe Carrotta/AP Photo/picture alliance

Wannan dabi'a ko kuma sana'a ta sayar da wasu sassan jikin al'umma ba wai matsala ce da ta tsaya a kan masu yi kadai ba, har da hadin kan likitoci da miyagun mutanen da ke sace jama'a gami da ma 'yan siyasa, a watannin baya aka kama wani tsohon sanatan Najeriya Ike Ekweremadu da matarsa bisa laifin safarar wani mutum har kasar Burtaniya da zummar sace wani sassan jikinshi ba tare da izininshi ba.

A yayin da wasu kan fada hannun miyagun mutane ko kuma ake tilasta musu, a kasar Kenya matasa da dama na kai kansu domin sayar da kodarsu daya. Willis Okumu mai bincike a cibiyar nazarin tsaro da ke kasar Kenya ya ce ba dukkanin sayar da wasu sassan jikin mutane ba ne ake yi ba bisa ka'ida ba ko kuma ya sabawa doka.

Wasu Matasa 'yan Brazil da suka je sayar da kodarsu a Afirka ta Kudu na yin nadama
Wasu Matasa 'yan Brazil da suka je sayar da kodarsu a Afirka ta Kudu na yin nadamaHoto: epa/dpa/picture-alliance

" Ya ce na tuna ganin wasu matasa da ke dauke da tabo a cikinsu wanda ke nuna sun je an cire musu koda daya. na damansu idan suka tafi wajen sayar da sassan jikin nasu su kan dawo ne da makudan kudade, a kalla dalar Amirka dubu shidda kwatankwacin Naira miliyan 10 kenan"