SiyasaAfirka ta Kudu
Afirka ta Kudu: Tankiya a kan rabon mukaman gwamnati
June 24, 2024Talla
Sai dai a cikin 'yan kwanakin nan, jaridun kasar, sun ba da rahoton samun tashin hankali a tattaunawar da ake yi tsakanin jam'iyyar ANC da babbar jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance DA ta 'yan Liberal. A cewar wadannan bayyanai cikin kusan mukaman ministoci guda 30, Jamiyyar DA na bukatar samun goma yayin da ANC ta ce za ta iya ba su mukamai biyar ne kawai. A Afirka ta Kudun gaba daya jam'iyyun siyasa goma ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa musamman ANC. da DA da wasu kananan jam'iyyu siyasa.