1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin cutar Covid-19 sun yi tarnaki a Afirka

Zainab Mohammed Abubakar SB
December 10, 2021

Matsaloli da hanyoyin dakile Omicron da ke zaman sabon nau'in cutar Covid-19 a nahiyar Afirka sun dauki hankali jaridun Jamus gami da annobar cutar zazzabin cizon sauro.

https://p.dw.com/p/445r7
Australien Covid-19 | Reisebeschränkungen wegen der Omikron-Variante
Hoto: Loren Elliott/REUTERS

Jaridar Neuer Zürcher Zeitung ta rubuta mai taken "Sabon nau'in Omicron ya jefa masu bincike cikin rudani". Jaridar ta ce wannan sabon nau'i na corona na yaduwa cikin sauri fiye da na baya. Sannan kuma tuni aka samu wani dangin Omicron da ke da wuyar ganewa.

A yanzu haka dai Omicron na ci gaba da yaduwa kamar wutar jeji idan ka kwatanta da sauran nauo'i da suka bayyana a baya, ba wai a kasar Afirka ta kudu kadai inda aka fara gano ta ba, amma har tsakanin wasu kasashen nahiyar Turai. Ra'ayoyin kwararru a fannin kimiyya jami'ar Bern ya zo guda kan matsayin Omicron. A cewar masanin cututtuka masu yaduwa Christian Althaus, wannan nau'in cuta ya samu samu yaduwa cikin sauri fiye da nau'in Delta da yanzu haka ya mamaye Turai.

Südafrika Covid-19 Impfstation DW Adrian Kriesch
Hoto: DW

A gundumar Gauteng da ke Afirka ta Kudu dai, Omicron na iya kama kaso 38 daga cikin dari a na al'umma a kowace rana, sai dai har yanzu babu sahihancin wannan adadi inji Althaus. Akwai alamu da ke nuni da cewar Omicron na iya kaucewa garkuwar jiki. Inda bayanai ke cewar wanda sukja kamu da corona a baya kan iya same kamuwa da Omicron. A cewar masana dai nan ba da jimawa ba Omicron zai maye gurbin Delta ba wai a Afirka ta Kudu kadai ba har ma a nahiyar Turai.

"Nahiyar Afirka na ci gaba da zama a baya, wajen samun alluran rigakafi" da haka ne jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta bude sharhin data rubuta a kan gaza jigilar rigakafin corona da Turai ta bai wa Afirka tallafi.

Jaridar ta ce Afirka na kara zama karen baya idan aka zo batun rigakagin COVID-19. A yayin da bayana hukumar nazarin ketare na Turai ke cewar, a yanzu haka wajen kashi 43 daga cikin 100 na al'ummar duniya ne aka yi wa cikakken allura, a Afirka kuwa kashi 7 kacal.

Idan har ana son cikanta muradun MDD na yi wa kaso 70 daga cikin 100 na al'ummar duniya rigakafin nan da watan Satumban shekara mai kamawa, wajibi ne a dauki matakin gaggawa na daidaita samar da alluran in ji wani jami'in tarayyar Turai a wannan Larabar. Ya tabo batun karancin wuraren adana da tafiyar hawainiya wajen amincewa da rigakafin da ma yadda mutane da yawa ke dasa shakku kan allurar ita kanta.

Malaria-Bekämpfung in Afrika | Kenia | Impfstoff Mosquirix
Hoto: Brian ONGORO/AFP

A yanzu haka dai EU ta bada gudummowar alluran rigakafi wajen miliyan 353 ga kasashe 'yan rabbana ka wadata mu, akasari ta karkashin shirin COVAX na MDD.

To sai dai a daya hannun kuma cutar zazzabin cizon saura na Malariya na cigaba da cin karenta babu babbaka a karshin inuwar COVID-19 a cewar jaridar Der Tagesspiegel. Rahoton hukumar lafiya ta duniya watau WHO ya nunar da yadda aka samu karin masu kamuwa da cutar Malaria. A kan haka ne samar da alluran rigakafin cutar ya karfafa wa likitoci gwiwa.

Jaridar ta ce kasashen Afirka na yankin kudu da Saharasun fuskanci koma baya sosai wajen yaki da cutar zazzabin cizon sauro. Bayyanar annobar corona ya assasa karuwar yawan marasa lafiya da ma mace mace, a cewar rahoton shekara shekara na WHO da aka gabatar a ranar Litinin.

Malaria-Bekämpfung in Afrika | Benin Verteilung von Moskitonetzen
Hoto: Yanick Folly/AFP

A shekara ta 2020, mutane miliyan 241 suka kamu da zazzabin cizon sauro, karin miliyan 14 idan aka kwatanta da shekara ta 2019. Yawan wadanda suka mutu ya haura daga dubu 70 tuwa dubu 627.

Babban darektan hukumar Lafiya Tedros Ghebreyesus ya ce tun kafin barkewar annobar corona, aka fuskanci koma baya wajen yaki da Malaria.

Sai dai duk da haka, godiya ga hukumomin lafiya na kasashen da zazzabin cizon sauro ke barna, saboda hasashen da aka yi Afirka na samun karuwar mace mace saboda corona bai zama zahiri ba. Kan haka ne  Ghebresesus ya jadada muhimmancin kara matsa kaimi wajen yaki da zazzabin cizon sauro.