1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona na raguwa a nahiyar Afirka

Binta Aliyu Zurmi MNA
August 27, 2020

Babban jami'i da ke hukumar kula da cututtuka masu yaduwa a Afrika John Nkengasong, ya ce nahiyar na samun raguwan masu kamuwa da cutar Covid-19 da kaso 20 cikin 100 a makonnin da suka gabata.

https://p.dw.com/p/3hakR
DW Sendung The 77 Percent
Hoto: DW

To sai dai babban jami'in na hukumar kula da cututtuka masu yaduwa a Afrika, John Nkengasong ya ce hakan ba yana nufin a koma gidan jiya ba ne domin wannan anobar ba a kai karshenta ba tukuna.

Masu aiko da labarai sun ruwaito jami'in na cewa gwaji da ma hanyoyin kariya da al'umma ke bi ana samun biyan bukata kuma yana da kyau a ci gaba da kiyayewa. 

Ya zuwa yanzu kasashen 23 daga cikin 54 a nahiyar Afirka sun sanar da samun raguwar masu kamuwa da cutar. Sama da mutane miliyan daya da dubu dari biyu ne ke dauke da cutar a Afirka wanda rabinsu ke a kasar Afirka ta Kudu.