1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus 21.04.2023

Usman Shehu Usman RGB
April 21, 2023

Jaridun Jamus sun mayar da hankali kan tashin hankalin da kasar Sudan ta fada a sakamakon barkewar rikicin siyasa da kuma matsalar tsaro a kasashen Mali da Tunisiya.

https://p.dw.com/p/4QPXz
Shugaban Sudan Abdel Fattah al-Burhan
Shugaban Sudan Abdel Fattah al-BurhanHoto: ASHRAF SHAZLY/AFP/Getty Images

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta fara labarinta kan rikicin kasar Sudan da cewa: Karfe biyar na safe aka fara kai hare-hare ta sama, yayin da sojoji da dakarun sa-kai ke fafatawa da juna a birnin Khartoum na Sudan, dubban daruruwan mutane sun makale, a takaice dai farar hula sun shiga wani tasku. Ita ma jaridar Die Welt ta yi sharhin kan kasar ta Sudan, amma ita kam ta duba mutane biyu da ke da alhakin yakin da kuma kasashen yamma. Jaridar na mai cewa, kasashen Yamma na bukatar dakatar da yakin da ke faruwa tsakanin janarorin soja da ke yakin neman hawa kan mulki. Ana sake samun fadace-fadacen zubar da jini a wata kasa ta Afirka saboda kasashen yamma sun ki fitowa su yi abin da ya dace.

Wadannan janarorin soja biyu duk kuwa da cewa kowa ya san suna da hannu a zubar da jini a kasar Sudan. A yanzu ko ya fahimci kwadayin mulki na wadannan sojoji da suka aikata laifin yaki tun a yakin Darfur. Janar Abdel Fattah al-Burhan da ke zama shugaban kasa da kuma mataimakinsa janar Mohammed "Hemeti" Daglo, duk cikin mutanen da ya kamata tuni an kai su kotu ta hukunta su bisa aikata laifin yaki, amma aka barsu a yanzu ga yadda suka jefa talakawa cikin ukuba, kuma yanzu sun sake aikata wani laifin yaki inda suke kai hare-hare a wuraren zama na fararen hula.

Pistorius da sojojin Jamus a Mali
Pistorius da sojojin Jamus a MaliHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Jaridar Die Tageszeitung  wace ta yi labari kan kasar Mali. Jaridar ta ce, nan ba da jimawa ba Jamus za ta janye rundunar sojanta daga Mali, amma ya kamata a ci gaba da yin hadin gwiwa a fannin raya kasa, ko da yake ba haka aka so ba, tunda ba wai yana nufin zaman lafiya ya samu ba. Ziyarar yankin tare da Ministan tsaro Boris Pistorius da Ministar raya kasashe Svenja Schulze hade da wasu jami’an gwamnatin Jamus sun ziyarci har yankin Gao don ganawa da sojojin Jamus da ke a kasar Mali, yayin da yanzu ake ce-ce ku-ce kan zaman sojan na Jamus a Mali. Yanzu kusan a fili ta ke zaman sojan Jamus a Mali lokaci kawai ake jira, amma gwamnatin Mali ta riga ta nuna cewa ba ta bukatar sojojin daga kasashen Turai. 
 
A sharhinta jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba dambarwar siyasar kasar Tunisiya ne, inda ta ce, an kama madugun 'yan adawa. A Tunisiya ana kallon Rached Ghannouchi a matsayin babban abokin hammayar shugaban kasar Tunisiya. Ga magoya bayan shugaba kasa Kais Saed, labarin kama madugun adawan wani abun murna ne da suka samu cikin watan ramadan, sai kuma wani labarin da ake ganin yana da nasaba da wannan kamun madugun 'yan adawa, wato ziyarar ministan harkokin wajen Siriya a Tunis, inda shi da takwaransa na Tunisiya suka yi bikin dawo da huldar diflomasiya a tsakanin kasashen biyu, wanda aka yanke tun shekaru sama da goma bayan barkewar yakin Siriya, don zaluncin da ake ganin Bashar Al-Asad ya yi wa talakawansa, a yanzu yanan kasancewa bakin ciki ga ‘yan Tunisiya da suma ke fuskantar gwamnatin mai karya dokoki da mulkin ba sani ba sabo.

Dan hammaya  Rached Ghannouchi
Dan hammaya Rached GhannouchiHoto: FETHI BELAID/AFP