1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka

January 22, 2021

Zaben da aka gudanar a kasar Yuganda a ranar 14 ga watan nan na Janairu ya dauki hankalin jaridun Jamus a labarai da sharhunan da suka yi kan nahiyarmu ta Afirka a wannan mako.

https://p.dw.com/p/3oFsc
Uganda Wahl Robert Kyagulanyi Bobi Wine
Madugun adawar Yuganda Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi Wine karkashin daurin talalaHoto: Sumy Sadruni/AFP/Getty Images

Yuganda ta kasance cikin yanayi mai kama da na makoki bayan nasarar da Shugaba Yoweri Museveni ya samu. Wannan shi ne taken labarin da jaridar Die Tageszeitung ta rubuta kan zaben na Yuganda. Jaridar ta ce abin mamaki, kusan mako guda ke nan komai ya yi tsit a Kampala babban birnin kasar Yuganda. Ta ce birnin da aka sanshi da hada-hada da launuka iri dabam-dabam da wani zaman zullumi gabanin zaben, yanzu ya zama wayam tun bayan sanarwar cewa Museveni da ya shafe kimanin shekaru 35 yana mulki a kasar, ya yi nasarar lashe zaben da kashi 58.5 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada. 'Yan adawa sun ki amincewa da sakamakon zaben, sai dai babu abin da za su iya, dakarun tsaro sun yi wa gidan jagoran 'yan adawa Bobi Wine kawanya, an yi masa daurin talala a gidansa sannan ana farautar magoya bayansa. Ba a san dai abin zai iya faruwa a kwanaki ko makwanni masu zuwa ba. Sai dai akasarin mutane na fata ba za a shiga wani tashin hankali ba.

Shugaba na dindindin inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Ta ce Museveni wanda tun a shekarar 1986 yake mulki a Yuganda, ya sake lashe zabe. Ya shiga jerin shugabannin kama karya da ke ganin an kare tsarin mulkin dimukuradiyya, matukar su ne suka ci zabe. Sakonshi ga al'ummar kasar shi ne shi kadai ke iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samar da wadata a kasar. Jaridar ta ce idan za a yarda da wannan magana to ke nan dole sannu a hankali al'ummar Yuganda su fara shiga rudu, domin Museveni dan Adam ne mai rai kuma dukkan rai zai dandani mutuwa, ga shekerunsa ma sun haura.

Großbritannien London 2020 | Yoweri Museveni, Präsident Uganda
Shugaba Yoweri Museveni na mutu ka raba a Yuganda Hoto: Henry Nicholls/REUTERS

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan mako ta leka kasar Habasha tana mai cewa barazanar yunwa a yankin da ke fama da rikici a Habasha. Ta ce yayin da ake ci gaba da fada jefi-jefi a yankin Tigray, ayyukan kungiyoyin agaji sun fara kankama sannu a hankali. An dade ba a san yadda irin mawuyacin hali da dubun dubatan 'yan gudun hijira ke ciki ba a yankin mai fama da rikici. Sai a ranar hudu ga watan nan na Janairu, Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta samu izinin shiga sansanonin Mai Ani da Adi Harush da ke kudancin Tigray.

'Yan gudun hijira fiye da dubu 25 da asali suka tsere daga Iritiriya ke rayuwa a can. Ko da yake fadan bai shafe su ba, amma kayan abinci da Hukumar Samar da Abinci ta Duniya ta kai a tsakiyar watan Disamban 2020, duk sun kare, ana kuma bukatar sabbi cikin gaggawa, in ba haka ba dubban 'yan gudun hijirar za su rasa abin sakawa a bakin salati. A ranar hudu ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata ta 2020, lokacin gwamnatin Habasha ta kaddamar da farmaki kan kungiyar 'Yantar da Al'ummar Tigray, kungiyoyin agaji sun bar yankin. Yanzu ne hukumar UNHCR ke kokarin sake girke ma'aikatanta a sansanonin 'yan gudun hijirar.