1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
September 11, 2020

A wannan makon, jaridun na Jamus sun mayar da hankali ne kan rikicin siyasar da ake a kasar Guinea da Mali da kuma batun coronavirus a kasar Benin.

https://p.dw.com/p/3iIrV
Guinea Präsident Alpha Condé
Shugaban kasar Guinea Alpha Condé Hoto: Getty Images/C. Binani

A wannan mako za mu fara sharhi da labaran jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta leka kasar Guinea da ke yammacin Afirka tana mai cewa, daga shugaba na gari zuwa dan kama karya, shugaban kasar Guinea Alpha Condé zai nemi wa'adin shugabanci karo na uku. Jaridar ta ce ko shakka babu Alpha Condé mai shekaru 82 zai sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar a zaben da za a gudanar a ranar 18 ga watan Oktoba, duk da jerin zanga-zangar adawa da wannan mataki da 'yan kasar suka kwashe tsawon makonni suna yi, abin da kuma ya yi sanadi na rayukan akalla mutune 30. 

Ganin kitse aka yi wa rogo

A cikin watan Fabrairu aka kwaskware kundin tsarin mulkin kasar domin bai wa shugaban damar yin ta-zarce bayan kammala wa'adin mulki sau biyu. Jaridar ta ce a 2010 lokacin da aka zabi Condé a matsayin shugaban kasar Guinea na farko bisa tsarin dimukuradiyya, an yi masa kallon mutumin da zai cire wa 'yan kasar kitse a wuta. Wani dan adawa a kasar ya ce da farko Condé ya nuna halin dattako shigen na Nelson Mandela amma daga baya ya mayar da kanshi Bokasa, wato tsohon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ya taba ayyana kansa sarkin sarakuna.
Daga Guinea sai kasar Mali da ita ma take a yankin na yammacin Afirka. A labarin da ta buga jaridar Der Tagesspiegel ta ce sojojin da suka yi juyin mulki a Mali sun yi galaba a kan kungiyar ECOWAS, a gwagwarmayar rike madafun ikon kasar. Ta ce a ranar Asabar da ta gabata hambararren shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita da aka yi masa juyin mulki a ranar 18 ga watan Agustan da ya gabata, ya bar kasar zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa inda za a yi masa magani na ciwon shanyewar wani bangare na jiki da ya kamu da shi. 

Mali CNSP Gespräche Putsch Malick Diaw
ECOWAS ta gaza tilasta sojojin Mali da suka yi juyin mulki, su mayar da mulkin nan takeHoto: Getty Images/AFP/M. Cattani

ECOWAs da AU sun gaza a Mali

Jaridar ta ce kungiyar ECOWAS da Tarayyar Afirka AU, sun bukaci sojoji su mayar da IBK kan karagar mulki, inda suka sanya wa Malin takunkumi domin matsa wa sababbin jagororin kasar lamba, amma daga bisani su kansu shugabannin kasashen Afirkan, sun gane cewa ba abu ne mai yiwuwa ba a sake mayar da Keita kan kujerar shugabancin kasar. A halin da ake ciki ma ECOWAS ta sassauto tana kuma kokarin ganin an sake gudanar da zabe a Mali nan da shekara guda, sannan farar hula su taka muhimmiyar rawa cikin gwamnatin wucin gadi, maimakon sojojin wadanda suka yi fatali da bukatar suna masu cewa sai bayan shekara biyu sannan za su mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula.
Gwajin cutar corona ya samar da makudan kudi ga baitul-malin gwamnatin Jamhuhuriyar Benin, inji jaridar Die Tageszeitung. Ta ce a lokacin matsalar annobar coronavirus gwamnatin ta yi dabara, ba ta kafa dokar kulle ba ba ta rufe kasuwanni da babban filin jirgin samanta da ke Cotonou babban birnin kasar ba. Mutane kimanin 2,190 suka kamu da corona a kasar daga cikin 40 sun rasu. Don ganin yawan bai karu ba, ta rufe iyakokinta na kan tudu, amma ta bar filin jirgin samanta a bude, inda aka rika gwajin kwayar cutar corona ga masu sauka kasar a kan kudi Euro 152 ga kowane fasinja, sannan masu barin kasar na biyan euro 75 da kuma Euro 38 na zaman jiran yin gwajin, a wani zauren alfarma da ke a airport din. Wannan dabara dai ta sama wa karamar kasar karin kudin shiga a lokacin na corona.

Benin Coronavirus Cotonou
Coronavirus ba sanya dakatar da harkokin kasuwanci a Jamhuriyar Benin baHoto: DW/Seraphin Zounyepke