1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan ta shirya kula da tsaron ƙasar da kanta

October 18, 2012

Shugaba Hamid Karzai ya ce ƙasarsa a shirye ta ke da ta ja ragamar tsaro da kanta domin tsarin da aka yi na mika ragamar kula da tsaron Afghanistan na tafiya yadda ya dace.

https://p.dw.com/p/16S6A

Mr. Karzai na waɗannan kalamai ne a wani taron manema labarai da ya shi da shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen a Kabul fadar gwamantin ƙasar ta Afghanistan inda Mr. Ramussen ya ce yunƙurin karɓar jan ragamar kula da sha'anin tsaron na ƙasar da mahukuntan na Kabul su ka ce sun shirya yi labarin ne mai daɗin ji ga ƙungiyar ta NATO.

A ƙarshen wannan watan da mu ke ciki ne dai dakarun na NATO za su miƙa wasu ɓangarori na ƙasar ga takwarorinsu na Afganistan,kazalika a cikin watanni masu zuwa NATO ta ce ta na tunanin miƙa ragowar ɓangarori biyun da su rage ga ƙasar yayin da ake sa ran barin ɗaukacin sojijin ƙasashen waje da ke Afghanistan a cikin shekara ta dubu biyu da sha huɗu.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Muhammad Nasir Awal