1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lafawar al'amura a Afghanistan

Abdul-raheem Hassan LMJ
August 17, 2021

Kura ta fara lafawa a Kabul babban birnin kasar Afghanistan, kwanaki kadan bayan da Taliban ta kaddamar da mulki tare da yin sassauci ga kowa.

https://p.dw.com/p/3z5of
Afghanistan PK der Taliban | Zabihullah Mujahid
Mai magana da yawun mayakan Taliban Zabihullah Mujahid Hoto: Rahmat Gul/AP Photo/picture alliance

Kungiyar ta nemi ma'aikata su koma bakin aiki tare da bude kofa ga mata a gwamnatin da ta kaddamar. 'Yan Taliban din dai sun yi kokarin kwantar da hankalin al'ummar kasar, bayan shiga rudani a babban filin jirgin saman Kabul domin neman tserewa. Kasashen duniya na iya ci gaba da kwashe mutanensu daga Afghanistan, bayan samun saukin tururuwar jama'a a titin jiragen sama da ke Kabul. Shugabannin kungiyar sun kuma gargadin sojojinsu kar su shiga gidajen mutane, kar su kuma saci dukiyar al'umma. Tuni dakarun Taliban din suka yi tsayin daka a dukkanin shingayen binciken da sojojin gwamnatin ke tsayawa, ciki har da hanyar shiga gidan gwamnati da kuma ofishin jakadancin Amirka da ke Kabul, suna kuma yin sintiri a cikin gari rataye da bindigogi suna daukar hotuna da mutane.

Afghanistan, Kabul | Checkpoint von Taliban Kämpfern in der nähe der US-Botschaft
Mayakan Taliban sun kame muhimman wurare, da a baya sojojin Amirka ke kula da suHoto: AP/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kungiyar Taliban da ta cika alkawuran da ta dauka na yin afuwa ga tsofaffin ma'aikatan gwamnati da bai wa mata damar zuwa aiki da makaranta, amma sanye da hijiabi. Sai dai da yake martani kan sukar kasashen yamma na zuba ido har gwamnatin kasar ta Afghanistan ta rushe bayan janyewar sojojin Amirka, Shugaba Joe Biden ya ce sakacin gwamnati ne da dakarunta kuma lokaci ya yi da Amirka za ta dau ki matakin rage kashe kudi kan sojojinta da ke waje kimanin shekaru 20. Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da mayakan Taliban da suka karbe iko kan mutunta hakkin dan Adam, da kuma samun damar ci gaba da aikin agaji ga fararen hula. A nata bangaren Rasha ta ce tabbacin da Taliban ta bayar na mutunta farar hula, alma ce ta fara samun nasara ga kasar.