1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dafifin mutane sun yi addu'a ga Janar Soleimani

Suleiman Babayo MNA
January 4, 2020

A birnin Bagadaza na kasar Iraki an yi zaman addu'a ga marigayi Janar Qassem Soleimani babban hafsan sojan Iran da Amirka ta halaka cikin wani farmaki ta sama a Iraki.

https://p.dw.com/p/3Vi88
Irak Bagdad Trauermarsch für Kassem Soleimani und Abu Mahdi al-Muhandis
Hoto: Reuters/W. al-Okili

Dafifin mutane a birnin Bagadaza na kasar Iraki sun halarci taron addu'a yayin da ake wucewa da gawar marigayi Janar Qassem Soleimani babban hafsa dakarun musamman na kasar Iran, wanda aka kashe sakamakon harin da Amirka ta kai a wannan Jumma'a da ta gabata. Mutanen sun hada da 'yan siyasa da masu karfin fada a ji.

Nan gaba zuwa wani lokaci za a mayar da gawar marigayin zuwa birnin Tehran na kasar Iran.

Tun farko Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce dakarun kasarsa sun halaka Janar Qassem Soleimani domin dakatar da yaki ba domin haddasa yaki ba, inda Shugaba Trump ya zargi marigayin da haddasa fitina a yankin.

Tuni dai Amirka ta gargadi 'yan kasarta su fice daga Iraki, yayin da kasashe irin su Holland da Faransa da Jamus suka nemi 'yan kasashensu da ke zaune a kasashen da ke makwabtaka da Iran da su yi kan taka-tsantsan. Yayin da Isra'ila babban mai dasawa da Amirka a yankin Gabas ta Tsakiya ta saka sojojinta cikin shirin ko-ta kwana.