1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da makamashin nukiliya a Japan

July 29, 2012

Masu adawa da amfani da makamashin nukiliya a Japan sun yiwa Majalisar dokokin kasar zobe suna rike da takardun da ke bayyana lahanin da makamashin ka iya janyowa al'umma

https://p.dw.com/p/15gBj
People display various signs as they stage a protest against the restart of Kansai Electric Power Co.'s Oi nuclear power plant in front of the Prime Minister's office in Tokyo, Japan, June 29, 2012. Tens of thousands of people congregated to voice their opposition to the government's decision to bring the idled No. 3 and No. 4 reactors at the Oi plant back into operation.
Hoto: picture-alliance/dpa

Dubun dubatan masu zanga-zanga waɗanda suke ɗauke da wutar kandir da ƙananan fitillu sun yiwa majalisar dokokin Japan zobe, a wani mataki na nuna adawa da makamashin nukiliya bayan bala'in da ya afku a tashar Fukushima bara.

Kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP ya ce aƙalla mutane dubu 10 suka halarci zanga-zangar suna sanyen da taguwa mai kama da irin na 'yan sama jannati.

Daga farko dai masu zanga-zangar sun gudanar da wani jerin gwano inda suka ɗaga kwalaye masu ɗauke da gargadi kan lahanin da makashin ka iya sake janyowa ga al'umma.

Wannan zanga-zanga na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da wani rahoton da gwamnati ta fitar kan rikicin makamashin na bara ya nuna cewa jami'an gwamnati da wasu ma'aikatar kamfanin wutar lantarkin ƙasar na TEPCO sun yi sakaci sosai wajen ɗaukan matakan kariya daga afkuwar hatsari.

To sai dai Kamfanin wutar ya wanke kansa inda ya ce ƙarfin girgizar ƙasar da ta janyo wannan bala'in ya wuce tsammani bare kowani irin mataki na kariya.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita:            Umaru Aliyu