Adamawa: 'Yan banga da dillancin makamai
March 11, 2016Ana dai zargin dan bangar ne da sayar da makaman ne ga 'yan fashi da kuma masu garkuwa da mutane gami da 'yan kungiyar Boko Haram ne a jihar.
Hakan dai ya fito fili lokacin wani samamen da fitaccen mafaraucin nan na arewacin Najeriya Ali Kwaraa ke yi a yankin kudancin jihar ta Adamawa, yankin da ke fuskantar radadin wata rigimar da aka zargi makiyaya da afkawa kabilar Bachama da haddasa asarar rayuka da kadarori a makwannin baya.
Kwamandan 'yan bangar da dubunsa ta cika, ya jingina hakan ne da neman kudin kula da motocin da gwamnati ta basu, da a cewarsa ke bukatar tayu da wasu kayayyaki, lamarin da jama'a da suka kafa alamar tambaya a kan haka.
Tuni dai wannan lamarin, ya fara daure kan jama'a da yanzu haka suke cikin farin cikin sakamakon samun zaman lumana a jihar da ta sha da kyar daga harkokin da suka shafi tabarbarewar tsaro.
Jagoran da ya ja tawagar da ta kaiga kama wannan dan bangar da ake zargi da sayar da makamai, wato Alhaji Ali Kwaraa, ya ce wannan sakaci ne na mahukunta ga harkar tsaro, yana mai shawartar gwamnati ta tsaya ga tsaftace harkokin banga da ya ce akwai jabu a cikinsu.
La budda dai, akwai bukatar azamar mahukunta ganin yadda aka soma yada labaran da ke da hadari ga tsaro a jihar da har yanzu ta ke fama da hajijiyar tashie-tashen mayakan tarzomar Boko Haram.