1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin masu zanga-zanga a Girka na karuwa

February 12, 2012

'yan sandan Girka sun yi ta arangama da masu zanga-zangar nuna adawa da sabbin matakan tsuke bakin aljihun da majalisa ke mahawara a kai da yammacin lahadi

https://p.dw.com/p/142I2
epa03100959 A protester covered with a Greek flag stands in front of the Greek Parliament in Athens, Greece, on 11 February 2012. Greek trade unions called a 48-hour general strike to oppose new austerity measures. During a planned vote on 12 February, the Greek Parliament will be asked to decide on the new bailout deal for Greece in the form of three separate articles - one for the PSI bond swaps to reduce Greek debt, one for the recapitalisation of banks and a third authorizing the prime minister and finance minister to sign the new loan agreement with Greece's creditors without detailing the measures involved. Greek trade unions meanwhile called for a 48-hour general strike and three days of mobilizations in protest of the new memorandum agreed with the creditors. EPA/SIMELA PANTZARTZI
Masu zanga-zanga da 'yan sanda a GirkaHoto: picture-alliance/dpa

'Yan sandan Girka sun yi amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zanga a farfajiyar majalisar dokokin kasar, inda wakilan majalisar ke shirin kada kuri'a a kan sabbin matakan tsuke bakin aljihun da shugaba Lucas Papademus ya gabatar musu.

'yansandan sun ce akalla masu bore dubu 15 suka kewaye majalisar, inda wakilan suka fara mahauwara yau da rana, a yayinda a wasu dubu 10 suka yi dandazo a dandalin Omonia wanda bai da tazara sosai daga majalisar.

Wannan zanga-zanaga, ya hada da kungiyoyin 'yan kasuwa, da kuma matasa wadanda suka yi askin kwal kobo suna fifita tutocin Girka, da kuma masu ra'ayin gurguzu da mabiyansu wadanda suka rufe fuskokinsu.

Masu zanga-zangar dai sun yi Allah wadai da abunda suka kira yaudara wanda kungiyar Tarayyar Turai da Asusun bada lamuni na duniya da babban bankin Turai suke so su yi ma kasar ta su.

A lokacin da ya bude taron 'yan majalisar Ministan kudin Girka Evangelos Venizelos ya ce yanma da mahimmancin gwamnatin ta sami goyon bayan wannan shirin domin ta samu kaso na biyu na euro milliyan 130 wanda aka alkawarta mata.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Abdullahi Tanko Bala