1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

2023: Wakilan jam'iyyu sun yi dandazo a Abuja

Uwais Abubakar Idris ZUD
May 19, 2022

Babban birnin Najeriya, Abuja, ya tumbatsa da masu zaben fitar da gwani da a cikin 'yan kwanaki masu zuwa za su zabi dan takarar da manyan jam'iyyun APC da PDP za su tsayar takarar shugaban kasa a zaben 2023.

https://p.dw.com/p/4BbA4
Nigeria Benin City | Edo State Wahlen | Godwin Obaseki gewinnt
Hoto: Olukayode Jaiyeola/picture-alliance/dpa

Wadannan 'yan siyasa da ke zama wakilan da za su zabi wadanda za su yi wa jam'iyyunsu takara sune a yanzu tutarsu ke kadawa a fagen siyasar Najeriyar, domin suke rike da sandar duka ta zaba wa kasar makoma. 

A baya dai yunkuri na kawar da amfani da wakilai a zaben fitar da gwani ya kasa samun nasara, abin da ya sanya su zama wadanda a yanzu ake masu kallon masu rike da akalar siyasar kasar kafin aje babban zaben shekara mai zuwa. Yawaitarsu a birnin Abuja, ta sanya tuni  manyan otel-otel suka zama matattara ta 'yan siyasa, inda 'yan takara ke bin su suna kamun kafa. Ana kuma zargin amfani da kudade a kokarin samun goyon bayan 'delegate' din a dukkanin manyan jam'iyyun kasar.

A bana ne dai Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya rattabu hannu kan dokar zabe, wacce ake sa ran za ta samar da gyare-gyare a wurin zaben fitar da gwani. To ko hakan za ta samar da sauyin da ake bukata a yanzu da ake 'yan kwanaki kafin a fara zaben fitar da gwanin? 

Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta bukaci jam'iyyun kasar su kammala zabukan fitar da gwanin nan da makon farko na watan Yuni mai kamawa.