1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu na Mu: Mata kan fada tarkon bauta a Saudiyya

Lateefa Mustapha Ja'afar YB
October 29, 2018

Wasu matan idan sun je aikatau baya ga duka ana zargin 'ya'yan Larabawa na lalata da su bayan iyayensu ma. Ga tsangwama da wasu ke sha.

https://p.dw.com/p/37Jyt
Beginn Pilgerfahrt Hadsch in Mekka 30.09.2014
Hoto: AFP/Getty Images/M. Al Shaikh

Shirin ya duba yadda mata 'yan Najeriya da ke zuwa aikatau Saudiyya ke cikin hali na garari. Mun samu zantawa da wasu mata guda biyu har da guda daga cikin agent-agent da ke yi wa mutane hanyar zuwa kasa mai tsarkin ta Saudiyya.

Hajiya Asma'u M. Bello da ta kwashe tsawon shekaru a Saudiyyan ta bayyana irin kalubalen da masu zuwa aikatau Saudiyya musamman mata ke fuskanta. Ta ce bisar da ake shigo da mata ya kamata a tsayar da ita daga Najeriya kasancewar wasu matan kan fada cikin halin cin zarafi ba ga 'ya'yan Larabawa ba har da iyayensu.

Abu na Mu: Mata kan fada lalata a Saudiyya

Alh. Umar Labaran Danga da ke da kamfanin Ummariyya Travelling and Tours a Najeriya, wanda shi ma agent ne ya ce su suna bin ka'ida wajen kai mutane kasar ta Saudiyya suna kuma bibiyar halin da suke ciki. Sai dai ya ba da shawarwari na mafita idan aka bi cikin gundarin shirin za a ji.