1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An karrama firaministan Habasha

December 10, 2019

An ba da lambar yabo ta  Nobel ta zaman lafiya ga firaministan Habasha Abiy Ahmed a birnin Oslo na Norway saboda rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasarsa da Iritiriya.

https://p.dw.com/p/3UYOf
Norwegen l Verleihung des Friedensnobelpreis an Abiy Ahmed in Oslo
Hoto: picture alliance/AP Photo/NTB scanpix/H. M. Larsen

A cikin watan Oktoba da ya gabata ne aka bayyana ba da lambar yabon ga firaministan na Habasha saboda rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasarsa da Iritiriya bayan da aka kwashe kusan shekaru 20 ana gwabza yaki tsakanin kasashen biyu wadanda ba su ko ga maciji. A shekara ta 2018 watannin uku kawai da zuwansa a kan mulki firaminista na Habasha Abiy Ahmed ya yi wata ganawa ta tarihi da shugaban Iritiriya Isaias Afeworki, a birnin Asmara domin farfado da zaman lafiya tsakanin kasashensu biyu.