1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A ƙasar Norway mutane 94 suka mutu a harin ta'addanci

July 23, 2011

Yayin da 'yan sanda suka ƙaddamar da binciken harin bam a Oslo da kuma harbin bindiga na kan mai uwa da wabi a tsirin Utoeya, shugabannin ƙasashen duniya sun Allah wadai da wannan ɗanyen aikin.

https://p.dw.com/p/1228b
Ma'aikatan agaji ke aikin ceto a birnin Oslo na ƙasar Norway.Hoto: dapd

'Yan sanda a ƙasar Norway sun baiyana ƙarin mutane da dama da suka rasu a harin kan mai uwa da wabi da wani ɗan bindiga daɗi ya yi jiya a tsibirin Utoeya dake arewa maso gabashin Oslo babban birnin kasar. 'Yan sandan sun ce ɗan bindigan wanda ya buɗe wuta akan gangamin taron matasa na jam'iyyar Labour a tsibirin na Utoeya ya bindige aƙalla mutane 80 har lahira ya kuma jikata wasu fiye da 90. Wasu waɗanda suka firgita sun yi ta faɗawa ruwa domin tsira da rayukansu.

Schießerei in Jugendlager auf der Insel Utoya
tsibirin Utoeya da ke ƙasar Norway,Hoto: dapd

An baiyana cewa ɗan bindigan wanda tuni 'yan sanda suka cafke shi ɗan asalin ƙasar ta Norway ne ana kuma tsammanin yana da alaƙa da wata ƙungiya ta masu tsatsauran ra'ayi. Harbin kan mai uwa da wabin ya biyo bayan wani harin bom ne wanda tun da farko ya auku a tsakiyar fadar gwamnatin a birnin Oslo a ranar juma'a wanda ya hallaka mutane bakwai da kuma jikata wasu da dama. Roger Burland wani ɗan jarida na gidan Talabijin ɗin ƙasar NRK wanda ya ganewa idanunsa al'amarin yace ko kadan a yanzu birnin bai yi kama da Oslo ba, tamkar dai wata ƙasa ce daban inda ake ganin irin wannan ta'asa. Firaministan ƙasar ta Norway Jens Stoltenberg ya wanda ya yi Allah wadai da harin ya yi kira ga jama'a sun zamo tsintsiya maɗaurin ki ɗaya. Harin dai na zama mafi girma a yammacin turai bayan harin da ya auku a Madrid na ƙasar Spain a shekarar 2004 wanda ya hallaka mutane 191.

A halin da ake ciki kuma shugabannin ƙasashen duniya na cigaba da yin Allah wadai da harin ta'addanci na ƙasar Norway. Ƙungiyar tarayyar Turai ta baiyana harin da cewa abin takaici a ƙasa kamar Norway wadda ta yi suna wajen zaman lafiya. Shugaban Amirka Barack Obama ya aike da saƙon ta'aziya ga gwamnati da kuma iyalan waɗanda suka rasu. Karamin Minista a ma'aikatar harkokin wajen Jamus Werner Heuer ya jajantawa ƙasar yana mai cewa Jamus za ta kasance da ita a kowane hali. Shima sakataren harkokin wajen Birtaniya William Hague a sakonsa na ta'aziya ya yitur da Allah wadai da dukkan ayyukan ta'addanci.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman