SiyasaIsra'ila
Isra'ila ta yi barin wuta a Gaza sa'o'i bayan sulhu da Hamas
January 16, 2025Talla
Ma'aikatar tsaron Falasdinu ta ce dakarun Isra'ila sun yi luguden wuta a wasu sassan Gaza tare da kashe fararan hula 7 a yayin da wasu gommai suka jikkata, kwana daya bayan sanar da kulla yarjejeniyar tsagaita buda wuta a tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.
Karin bayani : Isra'ila da Hamas sun cimma tsagaita wuta a Gaza
A cikin wata sanarwar da suka fitar, hukumomin yankin Falasdinu sun ce an kai harin ne a wata unguwa mai suna Rimla da ke tsakiyar Gaza. Ko a wannan Laraba, sai da hukumomin yankin Gaza suka tabbatar da mutuwar fararen hula 20 a wani barin wutar da dakarun Isra'ila suka yi wa yankin, sa'o'i a gabanin sanar da cimma yarjejeniyar sulhu.