1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A cimma matsayar kafa gwamnati a Kwango

Mouhamadou Awal Balarabe
July 26, 2019

Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukaradiyya Kwango da Joseph kabila sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka ba tare da rabon manyan ma'aikatu kamar cikin gida ko na kudi ba.

https://p.dw.com/p/3Mnkg
DR Kongo  Kinshasa Vereidigung Präsident Felix Tshisekedi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Gamayyar jam'iyun siyasa da ke goyon bayan shugaban Kwango Felix Tshisekedi da kuma takwarta da ke goyon baya wanda ya sauka daga mulki Joseph Kabila sun sanar da cimma yarjejeniyar kafa gwamnati hadin gwiwa bayan kwashe watanni shida na tattaunawa tsakaninsu. Bangarorin biyu sun bayyana cewar sabuwar gwamnatin za ta kunshi ministoci 65, inda 23 za su fito daga bangaren shugaba Tshisekedi yayni da 42 za su zama na bangaren Kabila, lamarin da ke nuna cewa tsohon shugaba kasa ya fi samun kaso mai tsoka.

Sai dai bangarorin Tshisekedi da na Kabila ba su yanke shawara a kan wadanda za su rike manyan ma'aikatu ba kama daga na cikin gida har i zuwa ga na kudi da na ma'adinai. Amma cikin wata hira da yayi da kafofin watsa labarai na Faransa, Shugaban Kwango Felix Tshisekedi ya ce zai sa ido wajen zaban wadanda za su rike ma'aikatun da aka fi ji da su. Tun dai ranar  24 ga watan Janairu ne aka rantar da Felix Tshisekedi ba tare da ya yi nasarar kafa gwamnati ba.