9/11: Birnin New York, bayan shekaru 20
Shekaru 20 bayan harin 11 ga watan Satumba, an fara dangana, sai dai har yanzu akwai alhini mai tarin yawa a birnin New York. Ga kadan daga cikin halin da birnin ke ciki, birnin da bai taba gazawa wajen cimma buri ba.
Alhini cikin damuwa
Tun bayan bikin bude shi a shekara ta 2014, Gidan adana kayan tarihi na tunawa da harin 11 ga watan Satumba, ya karbi bakuncin miliyoyin masu ziyara. Yana tunawa da kimanin mutane 3,000 da suka halaka a harin da wadanda suka halaka a harin cibiyar kasuwanci ta duniya a 1993. Duk ranar 11 ga watan Satumba, dangi na karanta sunayen wadanda harin ya halaka. Masu yawon bude idanu ma na halarta.
Wuta na ci a Cibiyar Kasuwanci ta Duniya
Hoton yadda jirgi na biyu ya tunkari ginin cibiyar kasuwanci ta duniya da tuni ta kama da wuta ke nan, na zaman guda daga hotunan da suka tsaya a zukatan al'umma har yanzu. Kasa ta sa'a guda bayan jirgin ya doki ginin, ginin cibiyar ta rushe. A lokaci guda, jirgin sama na uku ya daki ginin ma'aikatar tsaron Amirka Pentagon da ke birnin Washington, DC. An kalli hare-haren kai tsaye a fadin duniya.
Mummunan firgici a tarihi da matsalolin da suka biyo baya
Osama bin Laden da kungiyar 'yan ta'addan al-Qa'ida da ya kafa, su ne ke da alhakin hari mafi muni a tarihin Amirka. Cikin watan Oktoban 2001 makonni kalilan bayan harin, Amirka ta kaddamar da yaki mafi tsawo ta hanyar kai hare-hare ta sama da jiragen yaki a Afghanistan. Fatanta shi ne tarwatsa al-Qa'ida. An halaka Osama bin Laden a garin Abbottabad da ke Pakistan, a watan Mayun 2011.
Sabon yanayin sararin samaniya
An yi ginin a tsohuwar harabar Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da aka ke kira "ground zero." Ginin mai tsayin mita 417, ya kere dukkan gine-ginen birnin New York, daidai tsayin tsohon ginin Cibiyar Kasuwanci ta Duniyar da aka tarwatsa a 2001. A ranar hudu ga watan Yulin 2004, ranar samun 'yancin kan Amirka aka fara ginin, kasa da shekaru 10 bayan nan a watan Mayun 2013, aka yi bikin bude shi.
Alhini da ilimi da fasahar gini
An sadaukar da gidan adana kayan tarihin da tunawa da harin na 11 ga watan Satumbar, ga adanawa da yin bincike da koyarwa kan harin da aka kai cibiyar kasuwanci ta duniya. Mai zanen gine-gine dan Isra'ila da Amirka Michael Arad ne ya zana. Duk shekara akwai miliyoyin masu ziyara. A 2018 kadai, sama da mutane miliyan uku sun je gidan adana kayan tarihin sama da miliyan shida wajen tunawa da harin.
Daukar hoto a ginin da ya rushe
Rayuwa ta koma kamar da a wajen da dubban mutane da ke da asali da addinai dabam-dabam suka halaka, shekaru 20 din da suka gabata. Masu daukar hotan kansu da masu yawon bude idanu da kuma masu alhinin, na hallara a wajen da ya sauya tarihin birnin New York da ma duniya baki daya.
Alhini da tunawa da wadanda suka halaka
A ranar 31 ga watan Agustan 2021, an saka dan karamin hoton Lauren Grandcolas domin tunawa da ranar haihuwarta. Ta rasu tana da shekaru 38, yayin da take cikin jirgin United Airlines Flight 93. Fasinjoji sun yi kokarin kwace jirgin, sai dai 'yan ta'addan sun tarwatsa shi a Pennsylvania. An yi ta bayar da labarin Grandcolas a matsayin guda cikin abin tunawa a harin 11 ga watan Satumbar 2001.
Abubuwan tunawa a cikin birnin
An yi gini a gabar ruwa ta Hudson da ke New Jersey, domin tunawa da harin 11 ga watan na Satumbar 2001 da barakuzan ginin cibiyar kasuwanci ta duniya. An dai yi ginin ne a wajen da aka ajiye wadanda aka ceto bayan harin. Yana daya daga cikin yankunan da ake alhinin tunawa da harin a birnin New York.
Shekaru 20 bayan harin
Shekaru 20 bayan harin: Birnin ya yi kukan asarar rayukan mutane sama da dubu 30 sakamakon annobar COVID-19 da kuma wasu da dama da suka halaka sanadiyyar mahaukaciyar guguwa. Sai dai birnin ya ci gaba da tsayawa da kafarsa. Har yanzu babu abin da ya sauya, kan yadda yake jan hankali.