1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɗaukar matakin doka akan jami'an tsaro a Masar

July 9, 2011

Hukumomin Masar sun tsare 'yan sanda uku bisa zargin kissar wani mutun ta hanyar cin zarafin sa

https://p.dw.com/p/11sKn
Zanga-zangar neman sojojin Masar su samar da sauyi da kuma hanzarta zartar da hukunci akan Hosni MuabrakHoto: picture-alliance/dpa

Hukumomin ƙasar Masar sun bayar da umarnin tsare wasu jami'an 'yan sanda guda ukku domin yi musu tambayoyi game da ƙarar da ta shafi wani mutumin da Iyalan sa suka ce azabtarwar da aka yi masa ne ta janyo mutuwar sa a hannun 'yan Sandan. Kamfanin dillancin labaran ƙasar ta Masar da ya ruwaito wannan labarin a wannan Asabar (09.07.11), ya ambata babban mai shigar da ƙara a yankin birnin Alexandria a matsayin tushen labarin.

A cikin watan Janairu ne jami'an tsaron Masar suka tsare Mohammed Sayyid Bilal - ɗan shekaru 32 da haihuwa, bayan wani bam daya tashi a ginin cocin da ba'a san wanda ya ɗana ba ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 23 a ranar ɗaya ga watan na Janairu. Yini guda bayan haka ne kuma jami'an 'yan Sandan suka miƙawa Iyalan Bilal gawar sa, wadda suka ce tana ɗauke da alamun azabtarwa da kuma ƙuna.

Kamfanin dillancin labaran na Masar ya ce binciken da aka gudanar ya gano cewar Bilal, wanda mabiyin Salafiyya ne, dake cikin waɗanda aka tsare bisa zargin, ba shi da wata alaƙa da harin da aka ƙaddamar akan cocin. Al'ummar ƙasar Masar sun zargi gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Hosni Mubarak da laifin gaza hukunta jami'an 'yan Sandan dake cin zarafin jama'a, kana a yanzu kuma majalisar wucin gadi ta sojojin dake mulki a ƙasar tana fuskantar matsin lambar kawar da matsalar cin hanci da rashawa da kuma gurfanar da waɗanda suka ci zarafin 'yan ƙasar a gaban ƙuliya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala