1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɓarkewar Cutar murar tsuntsaye a China

Zainab MohammedDecember 31, 2011

An gane kwayoyin cutar ne a jikin wani matukin Mota mai shekaru 39 da haihuwa a birnin Shenzhen

https://p.dw.com/p/13cIt
Eine vom Robert Koch Institut, RKI, am Dienstag, 28. April 2009, zur Verfuegung gestellte elektronenmikroskopische Aufnahme zeigt einen Influenzavirus des Subtyps H5N1. (AP Photo/RKI, Bannert) * NUR ZUR REDAKTIONELLEN VERWENDUNG BEI URHEBERNENNUNG: RKI * --- An undated electron microscopic image provided by the Robert Koch-Institute, RKI, in Berlin on Tuesday, April 28, 2009 shows an influenza virus of the subtype H5N1. (AP Photo/RKI, Bannert) * MANDATORY CREDIT * EDITORIAL USE ONLY *
ƙwayoyin H5N1Hoto: AP

Jami'an kiwon lafiya sun ruwaito sake ɓarkewar cutar murar tsuntsaye a kasar ta China, a karon farko da aka samu kwayoyin cutar a jikin bil'adama cikin watanni 18. Rahotanni sun ce a san samu kwayoyin cutar ta H5N1 ne a jikin wani matukin motar pasinja a garin Shenzhen mai cunkoson jama'a dake yankin kudancin China. Garin na Shenzhen mai yawan al'umma miliyan 10, na kan iyakar China da Hong kong ne. Honkong dai ta killace dubban kaji da dangoginsu, tare da haramta shigar da dangogin tsuntsaye cikin kasar, tun bayan samu kwayoyin cutar murar tsuntsayen ta H5N1a jikin kaji uku, a tsakiyar watan Disamban nan mai karewa.Duk da cewar cutar tana da mummunar lahani, hukumar kula da lafiya ta Majalisar Ɗunkin Duniya ta nunar da cewar babu barazanar yaɗuwar kwayoyin cutar tsakanin mutane, da ɓarkewarta a 2003. A yanzu haka dai hukumomin China da Hong Kong na aiki kafaɗa da kafaɗa domin shawo kan matsalar.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita : Usman shehu Usman