Ƙungiyar M23 na janye wa daga Goma
November 28, 2012Shaidu daga garin na Goma sun ce sun ga motoci da dama na ma'aikatun garin Goma waɗanda yan tawayen suka zara , suna ficewa da garin ɗauke da kayan abinci da kuma makamai,suna garzayawa a garuruwan Rutshuru da Rumangabo da ke a arewacin Goma inda suke da sansani;Omar Fikiira wani ɗan majalisar dokoki ne na arewacin Kiwu kuma ya tabbatar da gaskiyar zance.Ya ce ''har yanzu za a iya ganin motoci na wucewa suna yin saiti wajan Rutshuru inda nan ne cibiyar yan tawayen, ya ce kuma mun yi amanar cewar kamar yadda aka cimma yarjejeniya a Yuganda M23 za ta mutunta.
Shaidun sun tabbatar da ficewar yan tawayen
Daman tun can da farko babban kwamnadan na yan tawayen na M23 janar Sultani Makenga ya gayawa wata kaffa ta ƙasar waje cewar tun a jiya da yamma zasu fara tattara yana su yana su domin ficewa daga Gomar wanda ya ce kafin ranar juma'a sun kammala yin ƙauran baki ɗaya.
Addadin yan tawayen dai a yanki arewa maso gabashi na Kiwu ya kai dubu ɗaya da ɗari biyar, sannan kamar yadda aka cimma yarjejeniyar a ƙarshen wani taron da ƙungiyar ƙasashen yankin Grand Lac ta gudanar a birni Kampala na Yuganda a makon jiya, ta tanadi cewar dole ne yan tawayen.su janye daga Goma da kilomita 20,dan majalisar ya ci gaba da cewar da alama na ba da daɗewa ba komai zai daidaita.
Ya ce ''ni ina tsamani al'ummar Goma zasu kasance cikin natsuwa da kwanciyar hankali kuma dukanin ma'aikatun zas sake koma aiki ,ya ce na tabbata da zaran yan tawayen sun fice daga Goma ;gwamnatin jihar da majalisar zasu koma aKAn aikin su kamar da.
Yan tawayen na M23 galibi tsohin yan tawayen na ƙabilar tutsit wanda aka saka a cikin rundunar sojojin Kwang akan wata yarjejeniya da aka sa hannu a kai a cikin watan Maris na shekara ta 2009. Sun sake ɗaukar makamai a cikin watan Afrilu na wanan shekara,akan koken da suka gabatar cewar maimakon a watsa su ko'ina a cikin sasa daban daban na ƙasar domin gudanar da aikin soji ya kammata a bar su a yankin su na Kiwu da ke a gabashin domin kare iyalen su.
Al'umma na fuskantar barazana taƙaranci abinci a yanki na Goma
To sai dai kuma daga bisanni jagoran ƙungiyar Jean Marie Runiga ya ɓulo da wasu sabbin sharuɗan cewar tilas ne a gudanar da bincike akan wani yunƙurin kisa da aka so yi; akan wani ƙwarraran likitan Mukwege Denis; wanda ya yi sunna wajan ba da tallafi ga matan da aka yiwa feyɗe tare da ba da yancin yin walwala ga jagoran yan adawa Etienne Tshisekedi da kuma rusa hukumar zaɓe.Yanzu haka dai mutane kusan dubu ɗari biyar ne suka yi ƙaura daga garin Goma sakamakon tashin hankali, kana kuma matsalar ruwan sha na fomfi da wutar lantarki da magunguna da kuma abinci na iya ƙara dagulewa nan gaba, idan har al'amura basu daidaita ba saboda yawancin abinci da ake kai ;wa a sauran yankunan ƙasar ana fitar da shi ne daga Goma.
Hukumomin Kwango na zargin Ruwanda da Yuganda da tallafa wa 'yan tawayen
Ƙasar dai ta Kwango daman ta yi fama yaƙin basasa har so biyu a can baya a shekarun 1996 zuwa 1997 da kuma shekarun 1998 zuwa 2003 wanda ƙasar ta riƙa samun tallafi daga Angola a fadan da ta gwabza da ƙungiyoyin yan tawayen da ke samun goyon bayan Ruwanda da Yuganda da Burundi,a yanzu kuma Kwango da MDD na zargin Ruwanda da Yuganda da mara wa yan tawayen na ƙungiyar M23 baya.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi
Daga ƙasa za a iya sauraron wanan rahoto