Ƙungiyar EU ta yi suka ga matakan da Libiya ke ɗauka kan masu bore
February 23, 2011Shugabannin Ƙungiyar Tarayyar Turai, EU sun yi kira da a ƙaƙaba wa shugaba Muamnmar Gaddafi na Libiya takunkumi bisa amfani da ƙarfin tuwo da gwamnatinsa ke ci gaba da yi domin murƙushe zanga-zangar nuna adawa da shi. Shugaban majalisar ƙungiyar, Herman Von Rompuy ya ce wajibi ne a hukunta Gaddafi bisa yin amfani da ƙarfi. Ministocin harkokin wajen ƙasashen Jamus da Italy da Faransa da Spian da Birtaniya sun yi barazanar aza wa Libiya takunkumi .
Duk kuwa da Allah wadai da ake ci gaba da yi daga sassa daban-daban na duniya shugaba Gaddafi ya ƙi sauka daga karagar mulki. A cikin jawabinsa da ke zaman irinsa na farko tun bayan ɓarkewar zanga-zangar shugaban na Libiya ya lashi takobin ci gaba da zama a ƙasar har sai ya yi mutuwar shahada. Mutane ɗari uku ne aka ƙiyasce sun rasa rayukansu i zuwa yanzu. A don haka ƙasashe da dama sun fara kwasan 'ya'yansa daga Libiya. Hukumar zartarwar Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta kwashe 'ya'yanta kimanin dubu goma da a halin yanzu ke ƙasar ta Libiya kafin ranar Alhamis. Gwamnatin Turkiya ta ce tuni ta kwashe 'ya'yanta dubu biyar daga wannan ƙasa, China ita kuma a nata ɓangaren cewa ta yi tana jira ne Libiya ta ba ta izinin kwasan 'ya'yanata dubu 30 da jiragen sama na haya.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal