1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar ƙawance ta NATO zata kama aiki a Libiya

March 29, 2011

Barack Obama ya kare matakin sojan da ƙasashen ƙetare suka ɗauka a kan Libiya

https://p.dw.com/p/10jSP
Hoto: AP

Shugaba Barack Obama na Amurka ya kwatanta matakin sojan da ƙasashen ƙetare su ka ɗauka a kan Libiya a matsayin wani matakin da ya zo daidai da ƙudurin Amurka domin a cewar sa, rashin ɗaukar wani mataki dangane da rikicin zai zama tamkar cin zarafin talakawar ƙasar ne. Shugaban ya kuma ƙara da cewa, ƙungiyar ƙawance ta NATO zata kama aiki a Libiyan ne daga gobe laraba idan Allah ya kai mu. Obama, ya yi alƙawarin cewa a wannan karon aikin da za su yi Libiya ba zai ɗauki lokaci ba hakazalika ba zai ci kuɗi sosai ba kamar yaƙin da Amurka ta yi a Iraƙi. kamar yadda ya bayyana

"Jagorancin tabbatar da cewa an aiwatar da ƙudurin haramcin shawagin jiragen yaƙi da kuma kare fararen hulan da ke wurin zai koma wurin ƙawayen mu, kuma na tabbatar da cewa ƙawancen namu zai cigaba da matsin ƙaimi a kan raguwar dakarun na Gaddafi"

A jiya Litinin, Frime Ministan Burtaniya David Cameron da shugaban Faransa Nicolas Sarkozy suka fitar da wata sanarwar haɗin gwuiwa inda suke godo da dakarun da ke biyyaya ga Muammar Gaddafi, da su haɗa kai da dakarun 'yan tawayen ƙasar. Waɗannan dai na zuwa ne a gabanin taron ƙoli na ƙasa da ƙasa wanda za'a gudanar a yau talata a babban birnin London, wanda kuma zai haɗa wakilai daga ƙasashe 35. A halin da ake ciki dai 'yan tawayen na cigaba da dannawa zuwa garin Gaddafin wato Sirte

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Usman Shehu Usman