1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta yi kira ga shirya wani taro kann Somaliya.

October 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buhn

Ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta yi kira ga shirya wani taron ƙasa da ƙasa tare da Ƙungiyar Tarayyar Afirka, da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya, don tattauna batun samad da zaman lafiya a Somaliya.

Wani jami’in ƙungiyar ya ce babban sakatarenta Amr Moussa na son ganin an shirya taron ne kafin ƙarshen wannan watan, don sasanta rikicin Somaliyan, inda mayaƙan ƙungiyoyin islama da ke riƙe da babban birnin Mogadishu, ke ƙalubalantar gwamnatin wucin gadin ƙasar, a yunƙurin da take yi na yaɗa angizonta a duk faɗin Somaliyan.

Tun 1991 ne dai Somaliya ta kasance ba ta da gwamnati, bayan da madugan yaƙi suka hamɓarad da shugaba Mohammed Siad Barre, sa’annan daga bisani kuma suka dinga yaƙan juna. Masharhanta dai na ganin cewa, halin da ake ciki yanzu a ƙasar zai iya taɓarɓarewa ya zamo wani babban rikici wanda zai shafi duk yankin na ƙahon Afirka.