1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar ƙasahen larabawa na ƙara fuskantar matsin lamba

January 21, 2012

Ƙungiyar Larabawan na shirin ƙara tsawaita wa'adin tagawar wakilai masu saka ido a ƙasar Siriya da wata guda duk da irin sukar da take sha na gazawa

https://p.dw.com/p/13np9
Arab League Secretary-General Nabil Al Araby (L) and Qatari Foreign Minister Hamad bin Jassim talk during a meeting of the Arab States to discuss the report of a peace mission in Syria and ways to strengthen it, in Cairo, January 8, 2012. REUTERS/Asmaa Waguih (EGYPT - Tags: POLITICS)
Shugabannin ƙungiyar ƙasashen larabawaHoto: Reuters

Ƙungiyar ƙasashen larabawa na shirin ƙara tsawaita wa'adin tagawar wakilanta a ƙasar Siriya da wata guda duk da irin matsin lambar da take fuskatan.Sakamakon yadda ake yin suka dangane da yadda tawagar ta kasa dakatar da zubar da jinin da ake yi a ƙasar Siriya kusan watannin goma da suka wucce.

Nan gaba ne aka shirya shugaban tawagar ta masu saka ido akan siriya Mohammed Ahmed Moustafa -Al -Dabi zai gabatar da wani bahasi a birin Alƙahira wanda akan sa ne ƙungiyar za ta yanke shawara akan ci-gaban aikin tawagar. Kamfanin dillanci labarai na Faransa AFP ya ambato wani jami'in ƙungiyar Ali Jarouh ya na mai cewar za a ƙara tsaiwata lokacin da wata guda saboda wata ɗaya bai isa tawagar ta kammala aikinta ba .

Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala