Ƙoƙarin shawo kan rikicin Libiya
June 16, 2011Jakada na musamman da ƙasar Rasha ta tura zuwa ƙasar Libiya ya ce firaministan ƙasar ta Libiya ya bayyana masa cewar mahukunta a birnin Tripoli suna gudnar da tattaunawa tare da 'yan tawayen ƙasar dake da hedikwata a birnin Benghazi, tare da bayyana cewar ganawar tana gudana ne a can birnin Paris na ƙasar Faransa. Kamfanin dillancin labaran ƙasar Rasha ya ruwaito cewar gwamnatin shugaba Mouamer Gadhafi ta yi watsi da batun ya sauka daga muƙamin sa a lokacin wata tattaunawar da aka shirya a birnin na Tripoli a wannan Alhamis.
A halin da ake ciki kuma Ƙungiyar tarayyar Afirka ta gargaɗi Majalisar Ɗinkin Duniya cewar hare-haren soji a ƙasar Libiya, wani mummunan lamari ne dake wakana. Tuni dama taron ministocin ƙasashen Afirka ya buƙaci tsagaita buɗe-wuta domin bada damar warware matsalolin ta hanyar siyasa.
Jakadan Birtaniya a Majalisar Ɗinkin Duniya Mark Lyall Grant ya bayyana cewar, mai yiwuwa ba za'a tsagaita buɗe-wuta ba idan har shugaba Gadhafi bai yi murabus ba.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Ahmad Tijani Lawal