1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin samar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya

March 17, 2010

Ƙungiyar tarayyar Turai na taka rawa wajen ƙoƙarin sulhunta tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila

https://p.dw.com/p/MVAx
Catherin Ashton tare da Amr Musa.Hoto: AP

A yaune Kantomar kula da harkokin ƙetare a ƙungiyar Tarayyar Turai Catherin Ashton, ke gudanar da muhimmiyar tattaunawa tare da shugabannin Falasɗinawa da kuma na Isra'ila. Ashton zata fara yada zango ne a birnin Ramallah, domin ganawa da shugaba Mahmud Abbas na Falasɗinu, gabannin zarcewar da zata yi zuwa birnin Jeruisalem, inda aka shirya zata gana da ministan kula da harkokin wajen Isra'ila, Avigdo Liberman. A halin da ake ciki kuma, hukumomin Isra'ila sun ɗage zirga-zirgar da suka katse zuwa gaɓar tekun Jordan na tsawon kwanaki biyar, amma har ya zuwa wannan lokacin, ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar, bayan sanarwar da gwamnatin Isra'ila ta bayar na shirin gina sabbin matsugunsan yahudawa - 'yan kama wuri zauna a gabashin birnin Jerusalem. Ƙungiyar Tarayyar Turai, da Amirka da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya, dukkanninsu sun yi kakkausar suka ga matakin.

A halin da ake ciki kuma, Frime Ministan Isra'ila Benjamin Natanyahu, ya tattauna da shugaban Amirka Barak Obama, da kuma mataimakinsa Joe Biden - ta wayar tarho, a ƙoƙarin shawo kan taƙaddamar data kunno kai a tsakanin Amirka da Isra'ila bayan sanarwar da hukumomin Isra'ila suka yi na cewar, suna shirin gina wasu sabbin matsugunan yahudawa 1,600 - a dai-dai lokacin da mataimakin shugaban Amirka ke yin rangadi a yankin, da nufin shawo kan ɓangarorin biyu su koma kan teburin shawara - amma ba kai tsaye ba.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Yahouza Sadisou