1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin gamayyar Afrika wajen sasanta rikicin Libiya

April 11, 2011

Jacob Zuma na Afrika ta kudu ya ce Moammer Gaddafi ya amince da da yarjejeniyar tsagaita wuta da tawagar Afrika ta gabatar masa

https://p.dw.com/p/10rP3
Hoto: AP

Tawagar wakilan ƙungiyar Gamayyar Afrika ta isa birnin Benghazi domin tattaunawa da 'yan Tawayen Libiya, bayan cimma taswirar zaman lafiya da shugaba Moammer Gaddafi aTripoli. Bayan ganawarsu da gwamnatin ƙasar ta Libiya, Shugaba Jacob Zuma na Afrika ta kudu yace tattaunawar tasu ta haɗar da tsagaita wuta, samar da tsaro domin bada kayan agaji da tattaunawa tsakanin gwamnatin da 'yan Tawayen. Ganawar tasu dai ta samu amincewar Gaddafi a cewar Ramtane Lamamra na ƙasar Algeria, kuma shugaban komitin sulhu na gamayyar Afrika AU, " akan wannan batun na tsagaita wuta, shugaba Moammer Gaddafi ya tabbatar mana da goyon bayansa wa koƙarin komitin na ganin cewar an cimma tudun dafawa a koƙarin kawo ƙarshen yaƙin na Libiya, tare da aikewa da tawagar masu kulawa da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar"

Kawo yanzu dai 'yan tawayen Libiyan sunyi watsi da duk wata yarjejeniyar tsagaita wuta dazai bar Gaddafi ko kuma Dansa akan kujerar shugaban kasar . A halin da ake ciki kuma, wani samamen da ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ta kai wannan Lahadin a birnin Ajdabiyya, ya yi sanadiyyar lalata tankunan yaƙin Gaddhafi guda 26.

Mawallafiya: Zainab Mohammed abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal