1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙauracewa biyan Haraji

Umaru AliyuOctober 23, 2008

Matsalar ƙin biyan kuɗaɗen haraji

https://p.dw.com/p/FfKm
Ministan harkokin kuɗi na Jamus, Minister Peer Steinbrueck.Hoto: AP


A ko ina a nahiyar Turai, gwamnatoci suna shigar da kuɗaɗe masu yawan gaske domin ceto tsarin aiyukan bankunan su. A lokaci guda kuma, dubban miliyoyi sukan ɓace sakamakon boye su da ake yi a bankunan wasu kasashe a nan Turai, da basa karbar haraji mai yawa daga wadnanan kudade da aka boye. A yunkurin kawo karshen wannan mummunan hali ne ya sanya Faransa da Jamus suka gaiyaci sauran kasashe goma sha biyar na hukumar hadin kan tattalin arziki da raya kasashe, wato OECD, domin gudanarda taro na gaggawa a Paris. Ministan kudi na Jamus, Peer Steinbrück ya baiyana rashin jin dadin sa ga kasashen da basu amsa wannan gaiyata ba.


Yace ƙasashen da basu zo wnanan taro ba sune Luxembourg, Switzerland da Liechtenstein da Austria. Hakan kuwa zai sanya a rika yi mana, mu turawa kallo na rashin mutunci, saboda haka a gani na, muna da matsala a tsakanin mu.


Hukumar OECD ta tsara abin da ta kira kundi na kasash masu laifi dake karbar kudade na haramun suna boye su saboda kin biyan haraji. A wnanan kundi kuwa, kasashe ukku ne kawai aka lissafa, dukkan su kuma a nan Turai, cikin su har da Monaco, Andorra da Liechtenstein. Peer Steinbrück yace akwai akalöla kasa guda da ya kamata a sanya ta a wannan jeri, amma babu ita. Wannan kasa kuwa ita ce Switzerland.


Switzerland, inji shi, tana da sharuddan dakan zama gaiyata ga masu neman gujewa biyan haraji daga Jamus su kai kudaden su su boye a can, don su ki biyan haramin. Saboda haka Switzerland kamata yayi ta shiga wnanan kundi. Switzerlan din bata hada kai damu, sai idan an gano wata cuta ce ta kin biyan haraji. To amma kafin a tabbatardashaidar cutar kkin biyan haraji kan wani, tilas sai an sami cikakken bayani da Switzerland din take dashi amma bata bamu. Wannan ita ce matsalar.


A shekara mai zuwa hukumar ta OECD zata sabunta wnanan kuindi nata dake dauke da sunayen kasashen dake karbar kudaden haramun da aka boye domin kin biyan haraji. A lokaci guda kuma, za'a tsara wani kundin da zai kasance dauke da kasashen dake bayarda cikakken hadin kai domin gano irin wadnanan kudade na haramun. Ministan kudi na Jamus yana bukatar ganin an kara matsa lamba kan kasashen dake boye kudaden masu nemankaucewa biyan haraji, saboda a can ne kasuwnanin hada-hadar kudi masu hadari suke, wadanda kuma suna daga cikin wadanda suka haddasa rushewar al'amuran kudi a yanzu.


Ministan kudi Steinbrück yace idan har ba'a sami daidaituwa ko hadinkai na kasa da kasa ba, Jamus zata dauki mataki na kashin kanta. Hakan yana nufin kyautata matakan kula da harkokin kudi kenan da kuma karfafa hadinkai tsakanin hukumomin kula da harkokin kudin da jami'an kwasta. Yace za'a kyautata hanyoyi na sassauta haraji, to amma duk wanda yaki amfanida wannan gyara, to kuwa zai ji a jikin sa.