1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashen Turai zasu taimaka wa Spain

June 9, 2012

Kimanin Euro Biliyan dubu ɗari ne ake sa ran ƙasahen zasu baiwa Spain domin ta ƙarfafa jarin Bankunanta

https://p.dw.com/p/15BRC
A homeless person sleeps in the doorway of a bank in Madrid Thursday June 7, 2012. Spanish Prime Minister Mariano Rajoy pleaded with European leaders "to support those that are in difficulty" and push toward greater fiscal unity - a step that might allow its troubled banks to get direct financial help. The call comes although Spain insists it doesn't need outside aid. (Foto:Paul White/AP/dapd)
Hoto: dapd

Ministocin kuɗi na ƙasahen ƙungiyar Tarayyar Turai waɗanda suka tattaunawa ta waya tarlho, tare da shugabar Asusun ba da Lamuni na Duniya Christine Lagarde , sun ce mai yi wa su baiwa ƙasar Spain,agajin biliyan dubu ɗari a matsin kuɗaɗen ceto domin ta ƙara ƙarfafa jarin bankunanta waɗanda suke fama da basusuka.

Wannan agaji da ƙasahen zasu bayar wanda shi ne na huɗu ga wata ƙasa ta ƙungiyar Tarayyar Turai tun lokacin da aka soma samun matsalar tattalin arziki a nahiyar a shekara ta 2009.Bayan ƙasashen Girka da Irlande da kuma Portugal na zaman ceto na tattalin arziki mafi tarifi da ƙasahen suka yi.Nan gaba ne ƙasar ta Spain za ta gabatar da buƙatar samin kuɗaɗen ga ƙungiyar.Kuma wasu majiyoyin daga ƙungiyar sun ce matsayin Asusun ba da Lamuni na Duniya akan ƙasar ta Spain zai kasance na larwai ne kwai.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi