Ƙasashen larabawa sun yin Allah wadai da Siriya
September 6, 2012Shugaban ya baiyana haka ne a wajan taron ƙungiyar ƙasashen larabawa da ke ci gaba da gudana a birni Alƙahira na Masar, wanda taron kuma ya yi Allah wadai da kisan gilar da gwamnatin ke aiwatar wa a Siriyar.
Gidajan telbijan na duniya sun nuna hoton kujerar Siriya a zauran taron wanda babu wakilin ƙasar a zaune a kan ta, wanda ko a can baya kusan wata guda da ya gabata wakilin na Siriya a ƙungiyar ta ƙasashen larabawa ya ci gaba da wakiltar ƙasar sa.Wannan dai wani abu ne da ke nuna yadda ƙasar ta Siriya ke zama saniyar ware a cikin ƙasashen duniya, sakamakon yadda gwamnatin ta Bashar Al-Assad ke ci gaba da yin kunnen ƙashi a kan kiraye kirayen da ƙasashen duniyar suke yi na ta dakatar da kisan farar hular da sojojin gwamnatin ke yi.
Ƙasashen larabawa sun dage sai an sami canji a Siriya
A lokacin da ya ke magana a gaban wakilan na ƙungiyar ƙasashen larabawa shugaba Mursi ya ce tilas ne shugaba Assad ya yi marabus.Ya ce ''gwamnatin Siriya har yanzu ta na da sukunin dakatar da zubar da jini, ya ce ya kammata sun yanke shawara a daidai lokacin da ya dace kafin lokaci ya ƙure''.Wannan dai shi ne karo na farko da wani shugaban na ƙungiyar ƙasashen larabawa da ke yin kira ga takwaran sa da ya ajiye aikin shugabancin .Ƙungiyar ta buƙaci kwamitin sulhu na MDD da ya yi yunƙurin irin wanda ya yi a ƙasar Libiya na amfanin da ƙarfin sojan da ya kawo ƙarshen tsohuwar gwamnatin.
Damuwa ƙasashen a kan halin da jama'ar ƙasar Siriya suke ciki
Halin da ake ciki yanzu haka a ƙasar ta Siriya inda sama da mutane dubu ɗari suka ficce a cikin watan jiya zuwa ƙasashen maƙofta kamar yadda hukumar yan gudun hijira ta MMD ta baiyana ya kiɗimar da ƙasashen larabawan.Shugaban ƙasar Masar ɗin Mohamed Mursi wanda wannan shi ne karo na farko da ya ke yin jawabi a gaban taron ƙungiyar tun bayan da aka zaɓe shi a kan matsayin na shugaba; ya ce za a kafa wani kwamiti na shiga tsakanin na ƙasa da ƙasa waɗanda suka hada da Iran da Turkiya da Saudiyya da kuma Masar domin samar bakin zaren rikicin,kuma ya sha alwashin cewar zasu kawo sauyi a cikin ƙasashen larabawa.Ya ce ''Juyin juya halin da Masar ta yi ;ya ce ba wai kwai ba, na samar da yanci ne, da walwala na al'ummar ƙasar ba kaɗai; ya ce abu ne da zai zama jagora har ga sauran ƙasashen na larabawa''.
Sauyi dai ko da ƙarfi da alama ' yan addawa na Siriyar sun dage sai ya samu. Kuma a kwai rahotanin da ke nuna cewar a ƙasar ta Masar a gaban ofishin jakadancin Siriya an yi taho mu gama tsakanin jam'ian tsaro da yan addawar; na Siriya masu neman canza tutar ƙasar a ofishin da tutar juyin juya hali.
Mawallafi : Blaschke Björn/Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto