1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasar Sin ta yi kiran tsagaita wuta a Siriya

March 4, 2012

Yayin da ƙungiyar Red Cross ke shirin raba kayan agaji a Baba Amr na Siriya, ƙasar Sin ta buƙaci ɓangarorin da ke faɗa da juna su tsagaita wuta.

https://p.dw.com/p/14EnD
Syrian Red Crescent workers stand with the coffins of American journalist Marie Colvin, left, and French photojournalist Remi Ochlik at Assad hospital in Damascus, Syria, Saturday, March 3, 2012. Syrian Red Crescent officials handed over to embassy officials Saturday the bodies of two foreign journalists who were killed in shelling while trapped inside a besieged district in Syria's central city of Homs. (Foto:Muzaffar Salman/AP/dapd)
Jami'an Red Cross a SiriyaHoto: dapd

Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce tana fatan shiga birnin Homs a yau Lahadi domin kai muhimman kayayyakin taimakon jin ƙai ga jama'a, sai dai kuma har yanzu tana fuskantar tsaiko daga sojoji waɗanda suke datse jerin gwanon motocin dake ɗauke da kayan agajin, duk kuwa da sahalewar da gwamnati ta baiwa ƙungiyar. Wani mai magana da yawun ƙungiyar Red Cross a birnin Damascus, Saleh Dabbakeh yace sun damu ƙwarai da halin da jama'a ke ciki a Baba Amr da kuma sauran yankunan da sojoji suka yiwa ƙawanya a birnin Homs. A waje guda kuma rahotanni na cewa sojojin na Siriya sun yi ɓarin wuta a garin Qusair dake kan iyaka, lamarin da ya sanya jama'a ficewa da ƙafa. Ƙasar Sin wadda ita da Rasha sau biyu suna hawa kujerar na ƙi wajen daƙile ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya akan Siriya ta yi kiran gwamnatin Bashar al-Assad da kuma waɗanda ta kira ƙungiyoyin dake da ruwa da tsaki a rikicin su dakatar da buɗe wuta. Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama Human Rights Watch ta ce Kimanin mutane 700 ne suka rasu yayin da wasu dubban jama'ar kuma suka jikata a kwanaki 27 da aka yi ana musayar wuta a birnin Homs.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal