Ƙasar Mauritaniya, Sansanin bayi na ƙarshe
A Mauritaniya dake Arewa maso Yammacin Afirka, bauta tamkar yaye ne na zamani, ana hasashen kashi 10 zuwa 20 na al'ummar dake da yawan milliyan uku da rabi na rayuwa a ƙarƙashin tsarin dake amfani da wariya da ƙabilanci
Rayuwa cikin ƙunci
An haifi Schweda cikin bauta tare da ƙaninta Matallah a hamadar dake yankin Arewa maso Gabashin Mauritaniya. Da ƙyar da suɗin goshi Matallah ya kuɓutar da Schweda da 'ya'yanta tara(9) daga raɗaɗin bauta a watan Maris na shekarar 2013
Brinin ƙazanta
Fari na tsawon shekaru 25 ya sauya Mauritaniya daga al'ummar dake dogaro da kiwo zuwa na zamani. Wannan sauyi ko ɗaya bai zo da sauƙi ba, kuma kasancewar alƙaluma sun nuna rashin aikin yi, a kan kashi 40 cikin 100, yawancin 'yan ƙasa na rayuwa ƙasa da dalan Amirka guda ne kowace rana
Lallaɓawa
Ungwannin talakawa sun yaɗu daga wajen birnin Nouakchott, inda tsoffin bayi da kuma waɗanda fari ya tayar daga matsugunnensu suka je neman ingancin rayuwa, kuma a nan ne suka gina gidaje da kwano da wasu kayayyaki
Danniya a duk faɗin ƙasa
Ba a ƙauyuka kaɗai ake bauta ba. An haifi Mbarka cikin bauta, kuma ta yi rayuwarta tana aiki da wani hamshaƙin mai kuɗi a Nouakchott. A shekarar 2011 ta sami 'yancinta da tallafin wani sannanen mai fafutukar kawar da aikin bauta mai suna Biram Abeid da ƙungiyarsa ta IRA
Samun 'yancin walwala
Messaoud Boubacar (hagu) daga ƙungiya mai zaman kanta ta SOS Esclaves, shi ne ya yi mafarin samun 'yancin Matallah (dama) da ma na 'yar uwarsa da 'ya'yanta tara (9). Su biyun mambobin wani ɓangaren al'umma ne da ake ƙyama mai suna Hratine, kuma sun haɗa zuri'a da ƙabilun Afirkan dake zaune kusa da rafin Senegal waɗanda Larabawa suka ci su da yaƙi
Bayi masu fiskantar ƙyama
Hratine suna fama da wariya da tsangwama saboda rashin galihu. Babu nagartattun alƙaluman dake nuna yawansu a al'umma, amma ƙungiyoyin dake da rajin kare hakkin bil adama na ƙiyasin cewa kashi 10 zuwa 20 na al'ummar Mauritaniya dake da yawan milliyan uku da rabi bayi ne.
Al'umma mara mahaifi
"A bauta, mahaifi ba shi da mahimmanci kuma kasancewarsa ba ya tasiri" a cewar Massaoud Boubacar na ƙungiyar SOS Esclaves "babu wata rawar da mahaifi zai taka, domin shugabannin ne sukan mallaki matansu, kuma idan matan sun haifa musu yara sukan sayar da su ko kuma su yi duk abin da suke sha'awar yi da su.
Buƙatar adalci
Yarg mai shekaru 11 na haihuwa (dama) na ɗaya daga cikin tsoffin bayin da suka taɓa yin nasarar gurfanar da wanɗanda suka bautar da su, har aka hukunta shi bisa laifukan da ya aikata masa. An yankewa mutumin hukuncin ɗauri na shekaru biyu ma laifin da ya kamata a ce ya sami hukuncin ɗauri na aƙalla shekaru biyar zuwa goma
Talauci
Mauritaniya na ɗaya daga cikin ƙasashe masu arziƙi a yammacin Afirka, musamman wajen albarkatun kifi da na ƙarƙashin ƙasa, sai dai ba kowa ne ke cin moriyar arziƙin da ƙasa ke samu daga waɗannan albarkatu ba
Neman na kaiwa bakin salati
Iyalin Matallah, a nan matarsa da ɗansa - suna rayuwa cikin talauci, kamar yawancin 'yan Hratine da tsoffin bayi amma duk da irin ƙalubalen da suke fiskanta, sun riƙe mutuncinsu da kuma kyakyawar fata irin wanda ba safai ake ganinta ba, na cewar su ma da yardar Allah rayuwarsu za ta sauya nan gaba