Ƙaramin jakadan Italiya a Libiya ya sha daga hari
January 13, 2013Wasu mutane ne ɗauke da makamai da ba a tantance ko su wanene ba suka buɗe wuta a kan motar jakadan wacce harsashi ba ya iya hudawa. Jakadan Guido de Sanctis na yawo ne a cikin garin a lokacin da 'yan bindigar suka buɗe masa wuta, sai dai babu wani wanda ya samu rauni daga cikin waɗanda ke cikin motar. Wannan hari dai na zuwa ne watanni ƙalilan bayan harin da masu kishin addini suka kai a ofishin jakadancin Amurka wanda a kan sa, suka kashe jakadan da wasu mutane guda ukku.
Sanctis ɗan shekaru 51 da haifuwa na a birnin Benghazi tun lokacin da aka fara yin boren da ya kifar da gwamnatin Mouammar Kadhafi a shekara ta 2011 kuma a makon gobe aka shirya zai fara aiki a sabon mazaunin da aka kai shi a ƙasar Qatar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal