Ziyarar shugaban tawayen Libiya a Jamus
July 1, 2011Yayin wata ganawa da suka yi a birnin Berlin, ministan harkokin wajen Jamu,s Guido Westerwelle da shugaban 'yan tawayen Libiya sun tattauna ba da ƙarin taimako ga 'yan tawayen. Gwamnatin Jamus ta na mai da hankali ne ga ba da da goyon baya na siyasa da diplomasiya da kuma taimakon kuɗi ga 'yan tawayen da ke ƙoƙarin tuntsurar da Shugaba Muammar Gaddafi. Westerwelle ya ce wannan ya haɗa ne da kadarorin gwamnatin Gaddafi da ke bankunan Jamus da aka ƙiyasce sun kai euro miliyan dubu bakwai. Shugaban 'yan tawayen, Mahmud Jibril ya ce ya na mutunta shawarar da Jamus ta tsayar ta ƙin shiga aikin da dakarun NATO ke yi a ƙasar ta Libiya domin kare fafar hula. Ya kuma nuna gamsuwarsa da irin goyon bayan da Jamus ke bai wa majalisar wucin gadi ƙasar ta Libiya. Tun da farko gwamnatin Jamus ta yarda ta ba da taimakon makamai a hare-haren da NATO ke kaiwa kan Libiya.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu