Zanga-zanga a Hong Kong
February 9, 2016Talla
Masu boren dai sun yi fito na fito da jami'an tsaron ne don nuna rashin amincewarsu da matakin da hukumomi a kasar suka dauka na hana sayar da abinci a kan tituna.
'Yan sanda dai sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma yin harbi a iska don tarwatsa masu zanga-zangar daidai lokacin da suke jifansu da kwalabe da duwatsu.
Masu aiko da rahotanni sun ce an lalata motocin 'yan sanda da gine-gine a yankin Kowloon inda wannan lamari ya wakana, wanda ke zaman mafi muni da aka gani tun bayan da aka yi zanga-zanga ta neman girka dimokradiyya a kasar shekaru biyun da suka gabata.