Zaɓen ´yan majalisar dokoki a Benezuwela
September 26, 2010Talla
A yau al'uma a ƙasar Benezuwela ke kaɗa ƙuri´a a zaɓen 'yan majalisun dokoki wanda a ke sa ran
a ƙalla mutune miliyian 18 za su hallarci runfunan zaɓen domin zaɓen wakilai 165 na Majalisar.
Zaɓen wanda ke zaman zakaran gwajin dafi ga shugaba Hugo Chavez a yayin da ya rage shekaru biyu a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na gudana cikin tsatsaura matakan tsaro wanda kusan jami´an tsaro dubu 25 a ka baza a cikin biranen ƙasar.
Masu fashin baƙi a kan al´amuran siyasa na hasahen cewa Hugo Chavez ɗin zai iya samu rinjaye a zaɓen duk da irin halin da ƙasar ta ke ciki na taɓarɓarewar al´amuran tsaro d akuma tsadar rayuwa.
A karon farko dai, ´yan adawa na ƙasar wanda suka ƙauracewan zaɓɓuɓukan a shekara ta 2005 a wannan jiƙon za a kara da su.